Za a Sasanta, Kungiyar APC Ta Zubar da Makamanta kan Neman Tsige Ganduje
- APC ta fara samun saukin rikicin shugabanci bayan kungiyar jam'iyyar, reshen Arewa ta Tsakiya ta zubar da kayan yakinta
- Kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya na fafutukar cire Abdullahi Umar Ganduje daga mukaminsa saboda zargin rashin dacewa
- Bayan kafa kwamitin sulhu, shugaban masu fafutukar tsige Ganduje, Alhaji Saleh Zazzaga ya bayyana matsayarsa kan bukatarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Wutar rikicin APC na shirin mutuwa, bayan kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta dakatar da fafutukar da ta ke a kan shugaban jam'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje.
Matakin dakatar da fafutukar ya zo a daidai lokacin da kwamitin zartarwar jam'iyyar na kasa ya ke shirin gudanar da babban taron APC.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta dade ta na adawa da zaman Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar tun bayan nada shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar APC ta yi adawa da Ganduje
Kungiyar APC karkashin Alhaji Saleh Zazzaga ta bayyana nadin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar da cewa bai halatta ba.
Alhaji Saleh Zazzaga ya jagoranci gudanar da zanga-zanga, ya yi taron manema labarai domin jaddada rashin goyon bayansu da kuma danganawa da kotunan kasar nan.
Ƴan APC sun daina adawa da Ganduje
A sanarwar da shugaban kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ya fitar a ranar Laraba, Alhaji Saleh Zazzaga ya bayyana cewa ba wai da Ganduje su ke adawa ba.
Yace su na kokarin kare martabar Arewa ta Tsakiya ne domin ta sharbi romon jam'iyya, amma sun jingine batun biyo bayan kafa kwamitin sulhu a APC.
Kotu ta yi hukunci kan korar Ganduje
A wani labarin kun ji cewa babbar kotun kasar nan bisa jagorancin Mai shari'a Inyang Ekwo ta tabbatar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.
Mai Shari'a Inyang Ekwo ya bayyana cewa lamarin rikicin shugabancin APC batu ne da ya danganci cikin gida, saboda haka babu kotun da za ta yi kokarin tsige Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng