Karshen APC Ya Zo, PDP Ta Gama Shirin Karɓe Kujerar Wani Gwamna a Najeriya
- Mataimakin shugaban PDP na Kudu maso Yamma, Lukman Ajisafe ya ce yana da ƙwarin guiwar jam'iyyarsa za ta karɓi mulkin Ondo
- Jigon ya ce rikicin shugabanci da ya addabi PDP a matakin ƙasa ba zai shafi nasarar da za ta samu zaben gwamnan jihar Ondo ba
- Ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024, INEC ta za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo watanni bayan nasarar APC a zaɓen Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Jam'iyyar PDP ta ce rigingimun cikin gida da suka dabaibaye ta a matakin ƙasa ba za su hana ta samun nasara a zaben gwamnan da za a yi a jihar Ondo ba.
Mataimakin shugaban PDP na ƙasa (Kudu maso Yamma), Lukman Ajisafe, ya ce rikicin ba zai daƙile nasarar da jam'iyyar ta hango a zaɓen Ondo ranar 16 ga watan Nuwamba.
Mista Ajisafe ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da hukumar dillancin labarai ta ƙasa NAN ranar Talata a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta na ganin nasara a zaɓen gwamnan Ondo
Kamar yadda Punch ta ruwaito, Lukman Ajisafe ya ce suna da kyakkyawan fatan ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi zai kawo jihar Ondo a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan rikicin shugabancin da yake neman tadiye jam'iyyar PDP.
Ajisafe ya kara da cewa galibin ƴan Najeriya musamman mutanen Ondo suna da ƙwarin guiwar PDP za ta ceto su daga mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar nan.
Zaben Ondo: Yadda PDP ke shirin karɓe mulki
Jigon PDP ya ce:
"Muna ganin haske tun yanzu, ƴan siyasa na dawowa cikin PDP domin ba da gudummuwa wajen ganin jam'iyyar ta koma kan madafun iko.
"Ina da tabbacin PDP za ta lashe wannan zaɓen da za a yi (a Ondo) saboda dumbin goyon bayan da muke samu daga al'umma a kowace rana.
"Muna kira ga INEC da jami'an tsaro su tsaya tsakiya, su yi adalci, ka da su nuna ɓangaranci.
Ajisafe ya buƙaci majalisar tarayya ta gyara dokar zaɓe domin ba da damar tura sakamako ta intanet kai tsaye daga akwatunan zaɓe, in ji The Nation.
Gwamnonin PDP sun warware rikicin shugabanci
Kun ji cewa gwamnonin da suka ɗare mulki a inuwar PDP sun bayyana Umar Damagum a matasayin sahihin shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng