Kwankwaso Ya Yi Magana kan Rikicin NNPP a Kano, Ya Faɗi Shawarar da Ya Yanke
- Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba zai tsoma bakinsa a rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar a Kano ba
- Kwankwaso ya ce bai kamata a saka shi a lamarin da bai shafe shi ba, yana mai cewa shugaban NNPP ke da hurumin magana
- Tun farko dai rigima ta ɓarke a NNPP wanda ta kai ga dakatar da sakataren gwamnatin Kano da kwamishinan sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar ba zai ce uffan ba game da rikicin da ya dabaibaye NNPP a jihar Kano.
Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Miller road a Kano ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024.
Abin da Kwankwaso ya faɗa kan rikicin NNPP
Da ƴan jarida suka buƙaci jin ta bakinsa game da rikicin NNPP, Kwankwaso ya ce ba ya son tsoma baki kan abin da bai shafe shi ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba na son magana kan batun don Allah, kar ku sa ni cikin abin da bai kamata a ganni a ciki ba
Shugaban jam'iyya ya yi magana ya ƙara magana, to ku tuntuɓe shi," in ji Kwankwaso.
Yadda rigima ta kunno a jam'iyyar NNPP
Idan ba ku manta ba rikici ƴa ɓarke a NNPP reshen jihar Kano wanda ya kai ga dakatar da sakataren gwamnati, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri.
A cewar shugaban NNPP, Hashim Sulaiman Dungurawa, sun ɗauki wannan matakin ne saboda zargin jiga-jigan biyu da rashin biyayya ga jam'iyya.
Gwamna Abba Kabir ya shiga tsakani
Sai dai an samu labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zaman sulhu, ya sasanta Abdullahi Baffa Bichi ta fusatattun ƴan NNPP a mazaɓarsa.
Bayan haka kuma an ji Abdullahi Baffa Bichi na cewa babu hannunsa a ƙungiyar 'Abba zauna da ƙafarka," mai kokarin raba gwamnan da gidan Kwankwaso.
A halin yanzu dai Kwankwaso ya kame bakinsa kan wannan rikici, ya ce ba zai ce uffan ba.
Kano: Ƴan Kwankwasiyya sun koma APC
A wani rahoton kuma ɗaruruwan 'yan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ne suka sauya sheka zuwa APC a ranar Talata.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya ce ya karbi daruruwan 'yan Kwankwasiyyar da suka sauya sheka a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng