Gwamnonin PDP Sun Raba Gardama, Sun Sanar da Sahihin Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa
- Gwamnonin da suka ɗare mulki a inuwar PDP sun bayyana Umar Damagum a matasayin sahihin shugaban jam'iyyar na ƙasa
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Talata
- Wannan na zuwa ne bayan kwamitin NWC ya dare gida biyu, inda ɓangare ɗaya suka naɗa Yayari Mohammed ya maye gurbin Damagum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum.
Haka nan kuma gwamnonin sun soke dakatarwar da aka yi wa kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba da mai ba da shawara kan harkokin shari'a Kamaldeen Ajibade, SAN.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamna Bauchi, Bala Mohammed ne ya sanar da hakan a safiyar ranar Talata, in ji Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Damagum: Gwamnonin PDP sun ɗauki matsaya
Da yake zantawa da ƴan jarida a Bauchi jim kaɗan gabanin kama hanyar zuwa Ondo, Gwamna Bala ya ce a halin yanzu sun amince kowa ya zauna a matsayinsa.
Damagum da wasu masu ruwa da tsakin PDP na tare da Gwamna Bala Mohammed a lokacin da ya sanar da haka yau Talata a Abuja.
Tun farko dai an naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum a wurin tarukan kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta ƙasa.
Sai dai NWC ya rabu gida biyu kuma kowane ɓangare ya gudanar da taronsa daban.
Yadda PDP ta naɗa Yayari Mohammed
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Yayari Mohammed ya ce NWC ya naɗa shi a matsayin muƙaddashin shugaban PDP ne domin dawo da martaba da ƙimar jam'iyyar.
Ya kuma tabbatar da cewa zai jagoranci PDP ba tare da nuna son rai ko wariya ga wasu ƴaƴan jam'iyyar ba.
Punch ta ruwaito cewa da yake hira da ƴan jarida a Abuja yau, Gwamna Bala ya ce:
"Mun warware rikicin PDP, gwamnoni, majalisar amintattu da sauran masu ruwa da tsaki sun amince NWC ta zauna a matsayinta, yanzu sun haɗa kansu babu sauraran hararar juna."
PDP ta naɗa shugaban jam'iyya a Kano
A wani rahoton kuma kun ji cewa PDP ta zabi Yusuf Kibiya a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na jihar Kano.
An ce Yusuf Kibiya ya yi nasara da gagarumin rinjaye inda ya samu kuri’u 3,964 yayin da ya doke abokin hamayyarsa Nura Nuhu wanda ya samu kuri’u 244.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng