'Ki Fita a Rayuwa Ta': Shehu Sani Ya Soki Matar El Rufai da Ta Gyara Masa Turanci
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya soki matar tsohon gwamnan jihar, Hadiza El-Rufai
- Sanatan da Hadiza El-Rufai sun kaure da cacar baki bayan matar tsohon gwamnan ta ci gyara Shehu Sani a rubutun Turanci
- Shehu Sani ya bukaci matar ta fita daga cikin lamuransa tun da yanzu ba su bibiyar juna a shafukansu na sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Matar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ta jawo cece-kuce a kafofin sadarwa.
Hadiza El-Rufai ta ci gyaran Sanata Shehu Sani bayan ya yi rubutu da Turanci a shafinsa na X.
Matar El-Rufai ta takali Shehu Sani
Matar tsohon gwamnan ta ci gyaran Sanatan ne bayan yada abin da ya wallafa kan maganar tsadar kaya a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya wallafa rubutu a shafinsa na X kan tafiye-tafiyen Bola Tinubu da ke da alaka da tashin farashin kaya.
Sanatan ya ce duk lokacin da Tinubu ya yi tafiya sai an samu karin farashin kaya da haraji.
"Sabuwar dokar tattalin arziki, idan Tinubu ya tafi ketare, haraji da farashin kaya sai sun tashi."
Wannan rubutu a cewar Hadiza akwai kuskure inda ta ci gyaransa kan wata kalma da ya rubuta ba daidai ba.
A kalamanta, ta ce bai dace wurin yin amfani da kalmar 'goes up' ba ya kamata ta zama 'go up'.
Sani ya yi martani ga Hadiza El-Rufai
Wannan gyaran bai yiwa Shehu Sani dadi da inda ya mayar mata da martani da cewa ta bar shi tun da yanzu ba su bibiyar juna.
"Na bar bibiyanki, kin bar bibiya ta amma har yanzu kina makale da ni, Mama ki bar ni haka nan."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya yabawa Matawalle kan ta'addanci
Kun ji cewa Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan yaki da ta'addanci.
Shehu Sani ya kuma bukaci al'umma da su bar sukar Matawalle da Nuhu Ribadu inda ya ce hakan na kawo cikas a yaki da ta'addanci.
Asali: Legit.ng