Bayan Shan Kaye a Zaben Edo, Dan Takarar Gwamna a LP Ya Dauki Sabon Mataki
- Dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar Labour (LP), Olumide Akpata ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba
- Olumide Akpata ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da tawagar lauyoyinsa da kuma masu ruwa da tsaki
- A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, Akpata ya yi cikakken bayani kan matakinsa da yadda aka yi zaben jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Olumide Akpata, dan takarar jam’iyyar Labour (LP) a zaben gwamnan jihar Edo, ya sake daukar sabon mataki bayan ya sha kaye a zaben da ya gabata.
Akpata ya yi ikirarin cewa an tafka kura-kurai a zaben na Edo kamar sayen kuri’u da kuma saba dokar tattara sakamakon zaben wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Duk da wadannan kalubale, jaridar The Cable ta rahoto cewa Olumide Akpata ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben jihar a kotu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Akpata na kin zuwa kotu
A wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, Akpata ya ce matakin da ya dauka na kin kalubalantar sakamakon zaben ya biyo bayan lissafin siyasa.
"Yayin da aka rufe kofar shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, mun tsaya a wani muhimmin mataki a jihar Edo da kuma dimokradiyyar Najeriya.
“Bayan tattaunawa mai zurfi da tawaga ta lauyoyi da masu ruwa da tsaki, na yanke shawarar kin kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a gaban kotun."
"An tafka kura kurai" - Akpata
Akpata ya ce kura kuran da aka tafka a zaben gwamnan jihar Edo ya zarce duk wanda aka taba gani a jihar a baya, inji rahoton Arise News.
Babban lauyan ya ce rashin bin ka’ida “alama ce ta gurbacewar tsarin siyasa” da ke addabar tsarin zaben kasar nan.
Ya ce:
"Wannan ba cin zarafin fasaha ne kadai ba, har ma da keta haddi na zamantakewa tsakanin gwamnati da wadanda ake mulka"
Sakamakon zaben gwamnan Edo
Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar INEC ta ayyana Monday Okpebholo, dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 21 ga watan Satumba.
Okpebholo ya samu kuri’u 291,667 inda ya doke Asue Ighodalo na PDP wanda ya samu kuri’u 247,274 yayin da Olumide Akpata ya zo na uku a zaben da kuri’u 22,763.
Asali: Legit.ng