Tsadar Rayuwa: Jam'iyyar NNPP Ta Ba Tinubu Mafita kan Halin Kunci

Tsadar Rayuwa: Jam'iyyar NNPP Ta Ba Tinubu Mafita kan Halin Kunci

  • Jam'iyyar NNPP ta samo mafita ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan taɓarɓarewar da tattalin arziƙin ƙasar nan ya yi
  • NNPP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya nemi taimakon tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kan halin da ƙasar nan ke ciki
  • Sakataren NNPP ya bayyana cewa a bayyane yake cewa gwamnatin Tinubu ba ta san hanyoyin da za ta magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya nemi taimakon tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Kiran ya zo ne kwanaki uku bayan da ƙungiyar kwadago ta Najeriya da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka yi kira da a soke ƙarin farashin man fetur da aka yi.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

NNPP ta ba Tinubu shawara
NNPP ta bukaci Tinubu ya nemi taimakon Jonathan Hoto: @DOlusegun, @GEJonathan
Asali: Twitter

NNPP ta caccaki gwamnatin Tinubu

A wata hira da jaridar Punch, sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dipo Olaoyoku, ya bayyana cewa a fili yake gwamnati mai ci ba ta da isassun dabaru kan yadda za a fitar da Najeriya daga cikin ƙunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren na NNPP ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta san hanyar da magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan ba.

"Game da batun Najeriya, babu abin da zai ƙara girgiza mu. Wannan gwamnati mai ci ba ta da hanyar magance matsalolin ƙasar nan."
"Idan aka samu rikici a ƙasar nan, sai a ka samu gwamnati mai neman mafitar wucin gadi kawai, hakan na nufin Najeriya sai abin da aka gani kawai."

- Dipo Olaoyoku

Wace shawara aka ba Tinubu?

Olaoyoku, ya ba da shawarar cewa idan dai har ba Tinubu ya nemi taimakon gogaggun masana harkokin mulki waɗanda suka samu ƙwarewa sosai rinsu Jonathan ba, to talakawa za su ci gaba da zama cikin ƙunci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Shugaban PDP ya bayyana masu shan wuya a gwamnatin Tinubu

"Za su iya roƙon Goodluck Jonathan ya taimaka masa kan yadda ya iya riƙe darajar Naira zuwa Dala a kan N200 kafin APC ta hau mulki. Su je su roƙe shi."

- Dipo Olaoyoku

Tinubu ya zarce Paris daga Landan

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Landan na ƙasar Burtaniya zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.

Shugaba Tinubu ya tafi birnin Paris ne a ci gaba da hutun aiki na kwanaki 14 da yake yi kafin ya dawo gida Najeriya ya ci gaba da jagorantar ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng