‘Yan Najeriya na Kallo,’ APC Ta Yi Magana kan Sauya Tsare Tsaren Tinubu

‘Yan Najeriya na Kallo,’ APC Ta Yi Magana kan Sauya Tsare Tsaren Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan kira da ake ga shugaba Bola Tinubu ya canza tsare tsarensa saboda matsalar tattalin arziki
  • Daraktan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim ne ya fitar da sanarwar a yau Juma'a inda ya ce suna kan gyara ne a Najeriya
  • Bala Ibrahim ya kara jaddada cewa jam'iyyar PDP ce ta lalata kasar nan a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulki daga 1999-2015

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta yi martani kan neman canza tsare-tsaren shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Hakan ya biyo bayan kira da jam'iyyar PDP ta yi ne inda ta ce tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu sun jefa al'umma a wahala.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

Bola Tinubu
APC ta yi magana kan tsare tsaren Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ne ya yi martani ga jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neman sauya tsare-tsaren Bola Tinubu

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta canza tsare tsaren da suka jefa al'umma a wahala.

Shugaban kwamitin amintattu, Adolphus Wabara ne yayi kiran yayin wani zaman jiga jigan PDP a birnin tarayya Abuja.

Martanin APC kan tsare tsaren Tinubu

Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ya yi martanin cewa duk mai neman canja tsare-tsaren Tinubu ya cire rai a kan hakan.

Bala Ibrahim ya kara da cewa tsare tsaren Bola Ahmed Tinubu suna kan hanyar kawo gyara ne a Najeriya.

Jam'iyyar APC ta zargi PDP da lalata Najeriya

Daraktan yada labaran APC ya yi zargin cewa gwamnatin PDP ce ta lallata kasar nan cikin shekaru 16 da ta yi.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Aminiya ta ruwaito cewa Bala Ibrahim ya ce a yanzu haka yan Najeriya suna ganin canjin da APC ta kawo kuma babu wata buƙatar sauyi da suke.

Yan siyasa sun caccaki tsare tsaren Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Laraba da ta wuce ne NNPCL ya yi karin kudin man fetur ana tsaka da wahalar rayuwa a kasar nan.

Lamarin ya tada kura musamman tsakanin masu karamin karfi kuma yan siyasa da kungiyoyi sun soki gwamnatin Bola Tinubu kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng