Rigima Na Neman Ɓarkewa a APC, An Dakatar da Tsohon Kakakin Jam'iyyar a Arewa
- Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a jihar Kwara, Alhaji Tajuedeen Aro bisa zargin cin amana
- Shugabannin APC na gundumar Ojumo ta Arewa maso Yamma ne suka sanar da haka a wata wasika da suka tura masa
- Da yake mayar da martani, Tajuedeen Aro ya zargi shugabannin jam'iyyar da ɗaukae mataki ba tare da bin ƙa'idojin da aka shinfida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau daɓkullum
Jihar Kwara - Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da tsohon sakataren yaɗa labaranta, Alhaji Tajuedeen Aro a jihar Kwara.
Shugabannin jam'iyyar na Ojomu ta Arewa maso Yamma sun zargi tsohon kakakin APC da cin amana da zagon ƙasa, shiyasa suka dakatar da shi.
Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 15 ga watan Satumba, 2024 wadda ta shiga hannun jaridar Daily Trust jiya Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa APC ta dakatar da jigon?
A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne domin daƙile yunkurinsa na kawo hargitsi da rabuwar kai a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar a matakin gunduma.
A wasiƙar da aka aika wa Alhaji Tajuedeen Aro, shugabannin jam'iyyar suka ce:
"Bisa zarge-zargen da ke kansa na cin amanar jam'iyya, yunƙurin haifar da sabani da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar da rashin girmama na gaba, mun yanke hukuncin dakatar da kai ba tare da ɓata lokaci ba."
Tsohon kakakin APC ta maida marani
Da aka tuntuɓe shi, tsohon kakakin APC a jihar Kwara, Alhaji Tajuedeen Aro ya tabbatar da samun wasiƙar dakatar da shi.
Sai dai ya musanta zargin cin amanar jam'iyyar, yana mai zargin shugabannin APC na gundumar da ɗaukar mataki ba tare da bin ƙa'idoji ba.
Jam'iyyar APC ta lashe zaɓen ciyamomi 16
A wani rahoton kuma hukumar zaben jihar Kwara (KWSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi.
Hukumar ta ce jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta yi nasarar lashe duka kujerun kananan hukumomi 16 da aka gudanar ranar Asabar.
Asali: Legit.ng