Tsohon Gwamna a Arewa Ya Gaji da Matsin Lambar EFCC, Ya Roƙi Tinubu Alfarma

Tsohon Gwamna a Arewa Ya Gaji da Matsin Lambar EFCC, Ya Roƙi Tinubu Alfarma

  • Ofishin yaɗa labaran tsohon gwamnan Kogi ya roki Shugaba Bola Tinubu ya sa baki a rikicin Yahaya Bello da hukumar EFCC
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da EFCC ta dage cewa sai ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu kan wasu zargi
  • Daraktan ofishin, Ohiare Michael ya yi zargin cewa EFCC na da wata ɓoyayyar manufa da ya kamata Tinubu ya sa a yi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Tsohon gwamnan jigar Kogi, Yahaya Bello ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicinsa da hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC.

Ofishin yaɗa labaɗai na tsohon gwamnan ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Tsohon gwamna, Yahaya Bello.
Ofishin yaɗa labaran Yahaya Bello ya bukaci Tinubu ya sa baki a fadan tsohon gwamnan Kogi da EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Me ya haddasa rikicin Yahaya Bello da EFCC?

Channels tv ta ce EFCC na neman Bello ne bisa tuhumar aikata laifuffuka da suka haɗa da cin amana, safarar kudi da wawure dukiyar al'umma da ta kai N80.2bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta sha nanata kira ga Yahaya Bello ya bi umarnin kotu, ya gurfana a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Sai dai tsohon gwamna ya yi zargin cewa ya fahimci hukumar EFCC na kokarin ganin ta wulaƙanta shi a idon duniya.

A sanarwar, daraktan ofishin yaɗa labaran Yahaya Bello, Ohiare Michael ya yi ikirarin cewa EFCC na da wata gurɓatacciyar manufa a aikin da take yi.

Yahaya Bello yana neman alfarmar Tinubu

Don haka ya buƙaci shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin bankado ainihin dalilan EFCC na matsawa Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta taso tsohon gwamna a Arewa, ana zargin ya 'sace' N110bn

"Muna kira ga mai girma shugaban kasa da ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan rigimar tsohon gwamna Yahaya Bello da EFCC, tun daga farko, da nufin gano hakikanin dalilan da suka sa ake son kama shi.
"Mun jinjina wa majalisar dokokin Kogi tare da godewa ‘yan Nijeriya da suka fahimci cewa EFCC na da wata manufa ta wulakanta Yahaya Bello.

- Ohiare Michael.

Tsohon gwamnan Kogi ba shi da laifi

A cewar Michael, tsohon gwamnan bai aikata laifin komai ba har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

Haka nan kuma ya ƙara da cewa duk wata tuhuma da EFCC za ta ratayawa tsohon gwamnan ƙarya ce matukar ba su gabatar da kwararan shaidu ba.

EFCC ta sake maka Yahaya Bello a kotu

A wani rahoton kuma Gwamnatin Tarayya ta hannun EFCC ta sake bankaɗo wata almundahana ta N110bn da take zargin da hannun Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

"Mun gano shirinsa," EFCC ta faɗi dalilin ƙin sauraron Yahaya Bello da ya miƙa wuya

Lauyoyin EFCC sun shigar da sababbin tuhume-tuhume 16 kan tsohon gwamnan na Kogi a gaban babbar kotun Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262