Bayan Shan Mummunan Kaye a Zaben Gwamna, Jam’iyyar LP Ta Ba Peter Obi Laifi
- Tsagin jam'iyyar LP ta taya dan takarar APC da ya lashe zaben Edo, Monday Okpebholo murnar nasarar zaben jihar
- Shugaban tsagin jam'iyyar, Julius Abure ya ce faduwar LP a zaben ba ta rasa nasaba da gudunmawar dan takararta, Olumide Akpata ya bayar
- Har ila yau, LP ta zargi dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Peter Obi da jawo mata rashin nasara inda ta zo na uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Shugaban tsagin jam'iyyar LP, Julius Abure ya zargi faduwarsu a zaben kan ɗan takara, Olumide Akpata.
Abure ya kuma zargi dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da ba da gudunmawa wurin kifar da jam'iyyar.
LP ta zargi Obi kan zaben Edo
Sakataren jam'iyyar Abayomi Arabambi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ta kuma taya zababben gwamnan na jam'iyyar APC, Monday Okpebholo murnar yin nasara a zaben.
Jam'iyyar LP ta yabi zaben gwamnan Edo
Ta ce wannan zabe da aka yi na daga cikin mafi kyawu da kuma adalci ba tare da wasu kura-kurai ba.
"Duk abin da INEC ta yi daidai ne, matsalarmu da shugabanni shi ne duk lokacin da abu mai mana dadi ba, to ba shi da kyau."
"Amma idan kuma ya zo a yadda muke so to ko ba shi da kyau za mu iya cewa hakan ya na da kyau."
- Abayomi Arabambi
Jam'iyyar ta ce son mulki da yaudara da kuma cin amana na Peter Obi da Gwamna Alex Otti su ne musabbabin faduwarta a zaben da aka yi a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.
Zaben Edo: Dan PDP ya fashe da kuka
Kun ji cewa bayan sanar da sakamakon zaben jihar Edo, jam'iyyar PDP ta cigaba da kokawa kan yadda aka gudanar da zaben.
Mataimakin daraktan kamfen dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya koka kan yadda aka tafka magudi a zaben da aka yi.
Emmanuel Odigie ya fashe da kuka ana tsaka da hira da shi a gidan talabijin inda jagoran shirin ya yi ta rarrashinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng