Ana Batun Zaben Edo, An Fara Shirin Dakatar da Gwamna daga Jam'iyya

Ana Batun Zaben Edo, An Fara Shirin Dakatar da Gwamna daga Jam'iyya

  • Jam'iyyar APGA ta fara shirin dakatar da gwamna ɗaya tilo da take da shi a cikin jihohin tarayyar Najeriya
  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar na zargin Gwamna Chukwuma Soludo da yiwa APGA zagon ƙasa
  • Shugaban APGA na ƙasa ya ce za su ɗauki matakin dakatarwar ne a kan gwamnan Anambra domin taka masa birki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar APGA, ya yi magana kan shirin dakatar da Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra.

Kwamitin na NWC ya bayyana cewa a shirye ya ke ya dakatar da Gwamna Chukwuma Soludo, tare da sauran masu hannu a yiwa jam'iyyar zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Jerin 'yan PDP daga Arewa da za su iya maye gurbin Umar Damagum

APGA na shirin dakatar da Soludo
Jam'iyyar APGA na shirin dakatar da Gwamna Soludo Hoto: Prof. Chukwuma Soludo
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar APGA na ƙasa, Cif Edozie Njoku ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa za a dakatar da gwamna Soludo?

Cif Edozie Njoku ya zargi Soludo da kawo cikas ga duk wani yunƙurin da kwamitin NWC wanda Kotun Ƙoli ta amince da shi ke yi na maido da jituwa a cikin jam’iyyar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Shugaban na APGA ya kuma bayyana cewa a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2024, kwamitin NWC, zai fitar da sunayen ƴan jam’iyyar da suka haɗa da Soludo, waɗanda za a dakatar da su saboda yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

"Wannan jam'iyya ce ta siyasa, kuma APGA za ta tsaya da ƙafafunta. Mun amince kan mutanen da za a dakatar daga jam'iyyar. Ɗaya daga cikinsu shi ne gwamna."

Kara karanta wannan

Daukar nauyin 'yan bindiga: Gwamna Dauda ya dauki mataki kan Matawalle

"Ina cewa shin za mu dakatar da gwamna ɗaya tilo da muke da shi. Amma idan gwamnan yana yi wa jam'iyyar zagon ƙasa fa? Dole ne mu taka masa birki."

- Cif Edozie Njoku

Gwamna Soludo ya kori kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya kori kwamishinansa na yaɗa labarai, Mista Paul Nwosu.

Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Soludo ya kori kwamishinan yaɗa labaran ne saboda rashin yin kataɓus a muƙaminsa tun bayan da aka naɗa shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng