"An Yi Mana Fashi da Tsakar Rana:" PDP Ta Soki Sakamakon Zaben Gwamnan Edo

"An Yi Mana Fashi da Tsakar Rana:" PDP Ta Soki Sakamakon Zaben Gwamnan Edo

  • Jam'iyyar PDP reshen Adamawa ta yi fatali da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ya ba dan takarar APC nasara
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana Monday Okpebholo a matsayin wandan ya doke jam'iyyun a zaben 2024
  • Shugaban PDP na Adamawa, Barista Ahmed Shehu, ya bayyana sakamakon da su ka aminta da shi, domin haka za a tafi kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Jam'iyyar PDP reshen jihar Adamawa ta bayyana takaicin yadda hukumar zabe ta INEC ta fitar da sakamakon zaben Edo.

A ranar Asabar din da ta gabata ne jama'ar Edo su ka gudanar da zaben da jam'iyyar adawa a jihar - APC ta yi nasara.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

zaben
PDP za ta nufi kotu kan zaben Edo Hoto: Asue Ighodalo-info
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa shugaban PDP a Adamawa, Barista Ahmed Shehu ya bayyana nasarar APC a matsayin fashi da tsakar rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben Edo: PDP na shirin garzayawa kotu

Jaridar Daily Post ta tattaro cewa Jam'iyyar PDP reshen Adamawa ta shawarci uwar jam'iyyar ta kasa da a gaggauta daukar matakin shari'a kan zaben Edo da ta ke ganin an tafka magudi.

Barista Ahmed Shehu, shugaban PDP na Adamawa ya jaddada goyon baya kan shirin da shugaban jam'iyyar na kasa, Umar Damagum ke yi na tafiya kotu kan sakamakon.

PDP ta yi watsi da sakamakon INEC

PDP ta ki amincewa da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta fitar kan zaben jihar Edo, inda Monday Okpebholo ya yi nasara da kuri'u 291,667.

Barista Ahmed Shehu ya bayyana cewa sakamkon da shugaban kwamitin yakin neman zabe a Edo kuma gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya tattaro shi ne daidai.

Kara karanta wannan

"INEC ba ta mutunta zabin mutanen Edo ba:" PDP ta ce an ci mutuncin dimukuradiyya

Jam'iyyar PDP ta zargi INEC da murde zaben Edo

A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta yi watsi da nasarar da hukumar INEC ta ce dan takarar APC, Monday Okpebholo ya yi a zaben da ya gudana a jihar Edo.

Mashawarci na musamman na yakin neman zaben PDP a jihar, Ayo Fadaka ya ce INEC ta yi kuskure wajen hana jama'ar Edo mutumin da su ka zaba ya wakilce su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.