Shugabancin PDP: Jerin 'Yan PDP daga Arewa da Za Su Iya Maye Gurbin Umar Damagum

Shugabancin PDP: Jerin 'Yan PDP daga Arewa da Za Su Iya Maye Gurbin Umar Damagum

  • Akwai yunƙurin da wasu jiga-jigan PDP ke yi na maye gurbin Umar Iliya Damagum daga shugabancin jam'iyyar
  • Masu son ganin an maye gurbin Damagum sun ce za a bar shiyyar Arewa ta Tsakiya ta kammala wa'adin Iyorchia Ayu
  • Legit.ng ta duba Gabriel Suswam da wasu mutum biyu a PDP ƴan asalin Arewa waɗanda za su iya maye gurbin Damagum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Akwai matsin lamba ga Umar Damagum domin ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.

A kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana cewa wasu gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na ƙasa (NWC) sun amince da cire Damagum daga muƙaminsa.

Kara karanta wannan

Damagum: Jerin gwamnoni 6 da ke goyon bayan a tsige shugaban PDP na kasa

Ana son maye Damagum daga shugabancin PDP
Kujerar Umar Damagum na fuskantar barazana Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Umar Damagum wanda ya fito daga yankin Arewa maso Gabas, na kusa ne ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana son maye gurbin Umar Damagum a PDP

Manyan PDP masu adawa da Damagum sun bayyana cewa ci gaba da zamansa a matsayin shugaban jam'iyyar ya saɓawa doka.

Sun bayyana cewa ya kamata a bar yankin Arewa ta Tsakiya ya kammala wa'adin tsohon shugaban PDP, Iyorchia Ayu wanda ya fito daga jihar Benue, cewar rahoton jaridar The Nation.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi duba kan jiga-jigan PDP guda uku da za su iya maye gurbin Damagum domin kammala wa'adin yankin Arewa ta Tsakiya.

1. Bukola Saraki

Bukola Saraki ya kasance shugaban majalisar dattawan Najeriya na 13 daga shekarar 2015 zuwa 2019.

An zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa ta takwas a ranar 9 ga watan Yuni, 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

Ya taɓa rike muƙamin gwamnan jihar Kwara daga shekarar 2003 zuwa 2011 kuma an zaɓe a muƙamin Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya a shekarar 2011, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Bukola Saraki ya sake lashe zaɓen Sanata a shekarar 2015 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Saraki ya bar jam’iyyar APC mai mulki ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP a shekarar 2018.

2. David Mark

David Mark tsohon Birgediya Janar ne na soja kuma gogaggen ɗan siyasa a Najeriya.

Ya taɓa zama shugaban majalisar dattawan Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2015 sannan ya kasance Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu daga shekarar 1999 zuwa 2019.

Kafin ya zama Sanata, David Mark ya taɓa zama gwamnan mulkin soja a jihar Neja daga 1984 zuwa 1986, kuma ya taɓa riƙe muƙamin ministan sadarwa.

Shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya da ya fi daɗewa a tarihi.

3. Gabriel Suswam

Gabriel Suswam tsohon gwamnan jihar Benue ne. Ya wakilci mazabar Benue ta Arewa maso Gabas a majalisar dattawa ta tara.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," Shugaban PDP na ƙasa ya faɗi matakin da za su ɗauka kan zaɓen Edo

Tuni dai Gabriel Suswam ya bayyana aniyarsa ta neman muƙamin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ciyamomi sun fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi na riƙon ƙwarya waɗanda Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a jihar Ribas sun fice daga PDP.

Kantomomin sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APP a lokacin da ake shirye-shiryen zaben kananan hukumomi ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng