“Bai Taba Cin Zabe a Edo ba;” Mataimakin Gwamna Ya Yi Shagube ga Gwamnansa

“Bai Taba Cin Zabe a Edo ba;” Mataimakin Gwamna Ya Yi Shagube ga Gwamnansa

  • Jigon APC kuma mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sake caccakar Gwamna Godwin Obaseki
  • Shaibu ya ce ko kadan bai rike Obaseki a zuciyarsa ba duk da abubuwan da suka faru a baya inda ya ba shi shawara
  • Ya ce gwamnan bai taba cin zabe ba sai da taimakonsu inda ya ce rasa karamar hukumarsa ya tabbatar da haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya sake dira kan gwamnan jihar, Godwin Obaseki.

Shaibu ya Obaseki bai taba nasara a zabe ba, ba tare da kasancewarsu da shi ba bayan sanar da sakamakon zabe.

Shaibu ya soki gwamnan PDP bayan faduwa zabe
Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya caccaki Gwamna Godwin Obaseki. Hoto: Philip Shaibu, Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Edo: Mataimakin gwamna ya yi masa shagube

Kara karanta wannan

'Dan PDP ya fashe da kuka a bidiyo yayin hira a gidan talabijin kan zabe

Jigon APC ya fadi haka ne yayain hira da Arise TV a jiya Litinin 23 ga watan Satumbar 2024 a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu ya ce faduwar Obaseki a karamar hukumarsa ga APC ya tabbatar da abin da yake fada a baya.

Ya ce bai da wata matsala kuma bai rike gwamnan mai barin gado a zuciyarsa ba kan abubuwan da suka faru, cewar rahoton Vanguard.

Har ila yau, Shaibu ya shawarci Obaseki da ya nemi gafarar yan jihar Edo duba da yadda ya kuntata musu.

Shaibu ya fadi silar faduwar gwamna Obaseki

"Abin da na ke fada ya tabbata, gwamnan da kansa ya gagara yin nasara a karamar hukumarsa, na yi nasara a mazabata da unguwa da kuma karamar hukumata."
"Ina sakamakon gwamnan? bai taba yin nasara ba a zabe, daman mu ne muke taimakonsa a kowane lokaci."

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya dura kan gwamna, ya ce ya mutu murus a siyasar Najeriya

"Abin da ya rage yanzu shi ne gwamnan ya nemi gafarar yan jihar Edo.'

- Philip Shaibu

Shaibu ya fadi silar faduwar PDP

Kun ji cewa mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya fadi wasu abubuwan da suka tattauna da gwamna Godwin Obaseki kafin zaben 2024.

Philip Shaibu ya ce wasu maganganu da gwamna Obaseki ya fada musu ne suka fusata wasu daga cikinsu kuma hakan ya yi tasiri a zaben.

Har ila yau, mataimakin gwamnan ya fadi yadda Adams Oshimhole ya kawo gwamna Godwin Obaseki kan kujerar gwamnan jihar Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.