IREV: Ana Daf da Kammala Daura Kuri'un Zaben Edo, An Kusa Sanin Sabon Gwamna

IREV: Ana Daf da Kammala Daura Kuri'un Zaben Edo, An Kusa Sanin Sabon Gwamna

  • Zaben gwamna a jihar Edo na 2024 na cigaba da ɗaukan hankula yayin da ake tattara kuri'un zaben gwamna daga ƙananan hukumomi
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta tattaro mafi yawan kuri'un da aka kada a kananan hukumomi a shafin yanar gizonta na IREV
  • A yanzu haka hankula sun fi karkata a kan yan takarar jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo da na jam'iyyar APC Monday Okpebholo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Yan Najeriya na cigaba da saka ido kan ganin wanda zai lashe zaben gwamna a jihar Edo.

A halin yanzu, hukumar zabe mai zaman kanta na cigaba da daura sakamakon zaben da aka tattaro a ƙananan hukumomi a shafin yanar gizonta.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke sakamakon zaben Edo da aka dora a IReV

Zaben Edo
Ana daf da tattara kuri'un zaben Edo a yanar gizo. Hoto Asue Ighodalo|Monday Okpebholo|Akpata Olumide Anthony
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan tattara kuri'un ne a cikin wani sako da hukumar zabe mai zaman kanta ta wallafa a shafinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An daura kuri'un zaɓen Edo kashi 98.58%

A daidai lokacin haɗa wannan rahoton, hukumar zabe mai zaman kanta ta daura sakamakon zaben Edo kashi 98.58% a shafinta na IREV.

Sakamakon zaben ya kunshi kuri'un da aka kada a dukkan ƙananan hukumomin jihar Edo a jiya Asabar.

Zaben Edo: Wuraren da suka tattara kuri'u

A halin yanzu, kananan hukumomi hudu ne a jihar Edo suka kammala daura sakamakon zabensu a shafin yanar gizon IREV na hukumar INEC.

Ƙananan hukumomin sun hada da Igueben, Esan ta Arewa maso Gabashin Edo, Esan ta Kudu maso Gashin Edo da kuma Owan ta Gabas.

Kuri'un da suka saura a daura a IREV

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa a cikin sakamakon zabe 4519 da za a daura a shafin IREV, an daura 4455.

Kara karanta wannan

'Dan acaba ya lashe kujera a APC da aka fadi sakamakon zaben kananan hukumomi

Hakan ya nuna cewa sakamakon na dab da kammaluwa wanda daga nan za a fara hasashen wanda zai zama sabon gwamnan jihar Edo a 2024.

Zaben Edo 2024: INEC ta tafi hutu

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ƙarin haske kan tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.

Kwamishin INEC na jihar, Anugbun Omuoha, ya sanar da cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen a yau Lahadi da zarar sun dawo daga hutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng