Edo 2024: Gwamna Ya Kaɗa Kuri'a, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci ga Hukumar INEC

Edo 2024: Gwamna Ya Kaɗa Kuri'a, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci ga Hukumar INEC

  • Gwamna Obaseki ya isa rumfar zaɓensa da ke makarantar firamare ta Emokpae a Benin, babban birnin jihar Edo kuma ya kaɗa kuri'arsa
  • Godwim Obaseki na jam'iyyar PDP ya bayyana gamsuwa da yadda zaɓen ke gudana tare da fatan hakan ya ɗore har lokacin tattara sakamako
  • Ya kuma yabawa al'ummar jihar Edo bisa yadda suka fito kwansu da ƙwarƙwata duk da ruwan da aka yi yau Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mai girma gwamnan Edo wanda wa'adinsa ke dab da karewa Godwin Obaseki ya kaɗa kuri'arsa a zaben gwamnan da ke gudana a faɗin jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Obaseki ya kaɗa kuri'a ne da misalin ƙarfe 11:57 na safiyar yau Asabar a rumfar zaɓe ta 19, gunduma ta 4 a Benin City.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Dan takarar APC ya cika baki bayan ya kammala kada kuri'a

Gwamna Obaseki.
Edo 2024: Gwamna Godwin Obaseki ya kaɗa kuri'arsa a zaben da ke gudana yau Asabar Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Na'urar BVAS ta tantance Obaseki

Kamar yadda rahoton Punch ta kawo, akwatun da gwamnan ya kaɗa kuri'arsa na cikin makarantar firamare ta Emokpae a Benin, babban birnin jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na'urar tantance masu ƙara kuri'a BVASt a tantance gwamnan ba tare da wani tangarɗa ba kuma ya ƙaɗa kuri'a a ƙasa da mintuna 10 bayan ya isa rumfar zaɓen.

Da yake zantawa da manema labarai a rumfar zaɓen, Godwin Obaseki ya ce ya gamsu da yadda zaben ke tafiya a halin yanzu.

Gwamna Obaseki ya yi fatan kammala zabe lafiya

Ya kuma bayyana cewa yana fatan yadda zaben ke gudana cikin nasara, idan an zo tattara sakamako a yi a gama cikin kwanciyar hankali.

Obaseki ya roki hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi, kuma ta tabbata an tattara sakamako lami lafiya ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Zaɓen Edo ya ɗauki zafi, ɗan takarar gwamna ya ƙoka kan bayanan da ake turo masa

Ya kuma yaba wa masu kada kuri’a da suka fito duk da ruwan saman da aka yi domin su zaɓi wanda suke so ya shugabance su, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Rigima ta ɓarke a wata rumfar zaɓe

A wani rahoton kuma kun ji cewa an dakatar da kada kuri'a a wata rumfar zabe da ke gundumar Orhionmwon da ke a karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo.

An ce matasan rumfar ne suka tayar da rigima bayan da suka gano jami'an INEC ba su zo da takardar rubuta sakamakon zaben ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262