Edo 2024: Ɗan Takarar PDP Ya Koka, Ya Hango Wata Matsala Ana Tsaka da Zabe

Edo 2024: Ɗan Takarar PDP Ya Koka, Ya Hango Wata Matsala Ana Tsaka da Zabe

  • Mai neman zama gwamna a inuwar PDP, Asue Ighodalo ya nuna damuwa kan yanayin tsaro a zaben da ke gudana a jihar Edo
  • Ighodalo ya bayyana cewa ya samu labarin ƴan sanda sun cafke wani ɗan PDP da wasu mutane ɗauke da makamai a Uromi
  • Yanzu haka dai zaɓe ya kankama a sassan jihar Edo duk da an samu jinkirin zuwan ma'aikatan INEC a akwatun ɗan takarar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Dan takarar jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya koka kan barazanar tsaro a zaben gwamna da ke gudana yanzu haka a jihar Edo.

Ighodalo ya kuma yi zargin cewa ƴan sanda sun cafke wani ɗan jam'iyyarsa a gunduma ta 8 Uromi.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: INEC ta yi magana kan dora sakamakon zabe a na'urar IReV

Asue Ighodalo.
Edo: Ighodalo ya bayyana damuwa kan barazanar tsaro ana tsaka da zabe Hoto: Asue Ighodalo
Asali: Facebook

Channels tv ta haƙaito ɗan takarar PDP na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A Uromi 3, an kama daya daga cikin magoya bayan mu sa'a guda da ta gabata da wasu mutane dauke da bindigogi. Haramun ne wani ya je da makami wurin zaɓe, hakan ya saɓawa doka.
"Amma sai ka ga mutane suna nuna halin ko-in-kula, suna zaluntar jama’a da kuma kokarin tsoratar da magoya bayanmu,” inji shi.

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton cewa jami'an hukumar zaɓe INEC ba su hallara ba akwatun zaɓen ɗan takarar gwamna na PDP.

Wakilin Channel ya ziyarci rumfar zaben ya ce babu alamun jami’an INEC da sauran masu wakilan jam’iyyun siyasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262