Zaben Gwamnan Edo: Dan Takarar Jam'iyyar APC, Okpebholo Ya Kada Kuri'arsa

Zaben Gwamnan Edo: Dan Takarar Jam'iyyar APC, Okpebholo Ya Kada Kuri'arsa

  • Sanata Monday Okpebholo, dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da yanzu haka ke gudana ya kada kuri'arsa
  • An ce Monday Okpebholo ya kada kuri'arsa wajejen karfe 10 na safiya a rumfa mai lamba 001, gundumar Uwessan da ke Esan ta tsakiya
  • Bayan ya kada kuri'ar ne dan takarar na APC ya so yin magana da manema labarai amma aka ga masoyansa sun shilla shi saman iska

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Dan takarar gwamnan Edo karkashin jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ya kada kuri'arsa a yayin da aka fara gudanar da zaben jihar.

A yau Asabar, 21 ga watan Satumbar 2024 hukumar zabe mai zaman kanta ta kas (INEC) ta kaddamar da zaben gwamnan jihar Edo.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

Dan takarar APC, Monday Okpebholo ya kada kuri'arsa a zaben gwamnan Edo
Edo 2024: Da misalin karfe 10 na safiya dan takarar APC, Sanata Okpebholo ya kada kuri'arsa.
Asali: Twitter

Dan takarar APC ya kada kuri'a

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, dan takarar gwamnan Edo na APC ya isa rumfar zabensa da ke gundumar Uwessan, karamar hukumar Esan ta tsakiya misalin 9:00 na safiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hoton da aka wallafa ya nuna Monday Okebholo a kan layin masu kada kuri'a inda ya ke tsumayin kada kuri'arsa a kwatinsa mai lama 001.

A rahoton da TVC News ta fitar misalin karfe 10:00 na safiya, an ce dan takarar ya samu damar kada kuri'arsa kamar yadda dokar zaben kasar ta tanadar.

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan jihar Edo ke gudana

Bidiyon Okpebholo bayan kada kuri'a

Bayan kada kuri'arsa, bidiyo ya nuna yadda 'yan jarida ke kokarin jin ta bakin dan takarar gwamnan lokacin da matasa suka mamaye shi.

An ga matasan suna jinjinawa dan takarar a cikin yarensu yayin da ya gaza yiwa manema labarai bayani har zuwa lokacin da bidiyon ya kare.

Kara karanta wannan

Edo 2024: PDP ta fara korafi, dan takara ya fadi makircin da APC ta shirya

Sanata Okpebholo na fatan ya zama gwamnan Edo bayan da ya yiwa al'ummar jihar alkawarin kawo sauye sauye da za su canja rayuwarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Abubuwa 7 game da Monday Okpebholo

Tun da fari, mun ruwaito cewa Sanata Okpebolo fitaccen dan siyasa ne kuma jigo a Edo wanda ya dade yana taka rawa wajen bunkasa rayuwar al'ummar jihar musamman na mazabarsa.

A matsayinsa na sanata, Okpebholo ya gabatar da kudirori da dama da nufin inganta ci gaban tattalin arziki, ababen more rayuwa da inganta ayyukan zamantakewa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.