Karkatar da Tallafi: Ɗan Majalisa Ya Fusata, Ya Shirya Maka Gwamna a gaban Kotu

Karkatar da Tallafi: Ɗan Majalisa Ya Fusata, Ya Shirya Maka Gwamna a gaban Kotu

  • Ɗan majalisar wakilan tarayya ya lashi takobin maka gwamnan Benuwai a kotu kan zargin da ya laƙaba masa na karkatar da tallafi
  • Hon. Terseer Ugbor ya ce ba zai tsaya yana kallo a ɓata masa suna ba, yana mai cewa zai nemi a biya shi diyyar N1bn
  • Gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Hyacinth Alia ta kama wata tirela maƙare da kayan tallafi, wanda ta yi zargin ɗan majalisar ya karkatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Hon. Terseer Ugbor mai wakiltar mazaɓar Kwande/Ushongo a majalisar wakilai ta ƙasa ya ɗauki zafi kan laƙaba masa zargin karkatar da kayan tallafi.

Ɗan majalisar wanda ya fito daga jihar Benuwai a Arewa ta Tsakiya ya buƙaci lauyoyinsa su shirya maka Gwamna Hyacinth Alia da gwamnatinsa a kotu.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NESG ya faɗi kuskuren Tinubu da ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala

Gwamna Alia na Benue.
Dan majalisar na shirin maka gwamnan Benue a kotu kan zargin karkatar da tallafi Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Hon. Ugbor ya shirya ɗaukar matakin shari'a kan kashin da aka shafa masa domin wanke kansa da dawo da ƙimarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisar zai nemi diyyar N1bn

A wata sanarwa da ya fitar jiya Jumi'a, ɗan majalisar ya ce zai kai ƙarar gwamnatin Alia ne saboda bata masa suna, kuma yana neman a biya shi diyyar N1bn.

Sai dai ya bayyana cewa idan ya ci nasara aka ba shi waɗannan kuɗi, zai yi amfani da su wajen ginawa ƴan gudun hijira sababbin gidaje a Kwande.

Matakin na Ugbor ya biyo bayan kwace wata babbar motar dakon kaya maƙare da kayan tallafi wanda gwamnatin jihar Binuwai ta yi a kwanakin baya.

Wane zargi gwamna ke wa ɗan majalisar?

Gwamnatin Benuwai ta ce ta karɓe motar ne bisa zargin cewa dan majalisar ya karkatar da kayan tallafin domin amfanin kansa.

Kara karanta wannan

Kumallon mata: Wata matar aure a Kano ta zuba 'fiya fiya' a abincin ɗan kishiyarta

Gwamna Hyacinth Alia ne ya sa a tsare motar wadda ta ɗauko kayan tallafin da ɗan majalisar ya samo daga hukumar NEMA, a Makurɗi, rahoton Daily Post.

Ugbor ya yi barazanar shiga kotu

Amma Ugbor ya ce zai ɗauki matakin shari’a don wanke kansa da kuma tabbatar da an saki kayan agajin domin amfanin al’ummar mazabarsa.

"Dangane da wannan na umurci tawagar lauyoyi na su duba zarge-zargen tare da daukar matakin da ya dace don kare ƙima ta, sannan mu nufi kotu," in ji shi.

Gwamna Alia ya soƙi manya a Benuwai

A wani labarin kuma Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ce al'umma ne suka zaɓe shi kuma su zai yi wa aiki ba wasu tsirarun mutane ba.

Gwamna Alia ya bayyana haka ne da yake hira da ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan ganawa da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262