Abubuwa 3 da za Su iya Jawo Jam'iyyar PDP Ta Faɗi a Zaɓen Gwamnan jihar Edo

Abubuwa 3 da za Su iya Jawo Jam'iyyar PDP Ta Faɗi a Zaɓen Gwamnan jihar Edo

  • A gobe Asabar, 21 ga Satumba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya zaben gwamna a jihar Edo da ke kudancin Najeriya
  • Za a fafata a zaben ne tsakanin yan takara 17 wanda uku daga cikinsu ne manya kuma sun fito ne daga jam'iyyun PDP, APC da kuma LP
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa guda uku da za su iya jawo jami'yyar PDP mai mulki a jihar ta sha kaye a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kammala shiryawa domin zaben gwamna a jihar Edo a ranar Asabar.

Yan takara uku ne suka fi daukan hankalin al'umma a zaben kuma sun fito ne daga jam'iyyun PDP, APC da LP.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

Zaben Edo
Abubuwa da za su iya kayar da PDP a zaben Edo. Hoto: @Aighodalo
Asali: Twitter

Legit ta haɗa muku rahoto a kan wasu abubuwa da za su iya kawo cikas ga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me zai iya sa PDP faduwa a zaben Edo?

1. Rikicin cikin gidan jami'yyar PDP

Jami'yyar PDP na fama da rikicin cikin gida musamman kan shugabancin jam'iyyar wanda a baya bayan nan ya karu.

Rikicin ya yi ƙamari wanda a halin yanzu gwamnonin PDP sun rabu gida biyu kuma ba a dauko bakin zaren warware rikicin ba.

Masana na ganin rikicin cikin gida na cikin abubuwan da suka saka PDP faduwa a zaben 2023 kuma a yanzu ma zai iya tasiri a zaben Edo.

2. Ƙoƙarin APC na karbe jihar Edo

Jami'yyar APC ta sha alwashin karbar mulki a jihar Edo a wuraren yakin neman zabe domin bunkasa siyasarta a Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Majalisar amintattun PDP ta shiga ganawar gaggawa

Hakan wata alama ce da ke nuna cewa jam'iyyar APC ba za ta yi wasa ba wajen yin shiri na musamman domin samun nasara a zaben.

3. Ƙarfi da guguwar jami'yyar LP

Jam'iyyar LP ta samu karɓuwa sosai a Kudancin Najeriya kamar yadda aka gani a zaben 2023 wanda hakan ya zama barazana ga PDP.

Ana ganin mafi yawan masu zaben LP magoya bayan PDP ne a baya saboda haka idan su ka zabi LP a Edo za su rage kuri'un da PDP za ta samu sai ya kasance ko LP ko APC ta samu nasara.

Asue ya yi alkawari kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake zargin juya wasu masu rike da madafun iko, dan takarar gwamnan PDP a jihar Edo ya sha alwashi.

Asue Ighodalo ya sha alwashin tabbatar da ya tsaya da kafafunsa ba tare da barin wasu su na juya shi kamar waina ba idan ya samu nasara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng