Edo 2024: Hankalin PDP Ya Tashi yayin da Jam’iyyun Siyasa 9 Suka Goyi bayan APC
- Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyun siyasa tara sun rusa tsarinsu tare da marawa APC da dan takararta baya a zaben Edo mai zuwa
- Kasa da awanni 48 a zaben jihar, jam'iyyun sun ce za su yi aiki tukuru domin ganin dan takarar APC, Monday Okpebholo ya samu nasara
- Jam'iyyar NRM, SDP, ZLP, APM, ADP, APP, Accord, YPP da kuma AA ne suka marawa APC baya a wani taron manema labarai da suka kira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Gabanin zaben gwamnan jihar Edo na 2024 da ke tafe ranar Asabar, jam’iyyun siyasa tara sun marawa jam’iyyar APC baya.
Wannan ci gaban ba karamar barazana ba ce ga PDP mai mulki a jihar da jam'iyyar Labour da ake ganin su ne manyan jam'iyyun siyasa a zaben.
Jam'iyyu 9 sun goyi bayan APC a Edo
Cif Sam Arase, shugaban jam'iyyar NRM reshen jihar Edo ne ya sanar da rushewar jam'iyyun tara da marawa APC baya a cewar rahoton jaridar Daily Post.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A madadin kungiyar jam’iyyun siyasa masu rijista a jihar Edo, Cif Sam ya bayyana cewa jam’iyyun sun fi son 'dan takarar APC kuma suna da yakinin zai samu nasara.
Jam'iyyun da suka marawa APC a jihar Edo sun hada da SDP, ZLP, APM, ADP, APP, Accord, YPP, AA da kuma jam'iyyar NRM.
Zaben Edo: APC ta kara samun karfi
Jam’iyyu sun bukaci hukumar INEC da ma daukacin al'ummar Edo da su gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba tare da yin kira ga jama'a da su fito baki daya su zabi APC.
Jam’iyyun sun umurci 'ya'yansu da su yi aiki domin ganin nasarar dan takarar APC, Sanata Monday Okpebholo a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa.
Jam’iyyu 17 ne dama INEC ta bayyana za su fafata a zaben gwamnan Edo, wanda aka shirya yi a ranar Asabar 21 ga Satumba, 2014.
Kalli bidiyon taron jam'iyyun a nan kasa:
'Wanda zai lashe zaben Edo' - Malami
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani matashin malamin addinin Kirista, Joel Atuma ya bayyana cewa wani dan takara da aka raina ne zai lashe zaben jihar Edo.
Malamin addinin ya ce ya hango yadda za a tafka shari'a kan zaben jihar a kotu amma kotun ba za ta iya sauya sakamakon zaben da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng