Edo 2024: Jerin Yan Takara 17 da Suke Neman Kujerar Gwamna
- A ranar Asabar mai zuwa hukumar zaben mai zaman kanta ta sanar da cewa za a gudanar da zaben sabon gwamna a jihar Edo
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta tantance adadin yan takarar da za su fafata a zaben tare da mataimakansu a dukkan jam'iyyu
- A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku adadin dukkan yan takarar, mataimakansu da wasu bayanai da suka shafe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Shirye shirye sun kankama yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Edo a ranar Asabar mai zuwa.
Yan takara 17 ne za su fafata daga jam'iyyu mabanbanta a zaben inda aka samu mace daya a cikinsu.
Jerin masu takarar gwamnan jihar Edo
Legit ta samo cikakken bayani kan yan takarar ne a cikin bayanin da hukumar INEC ta wallafa a shafinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Jami'yyar A ta tsayar da Iyere Kennedy dan shekaru 50 matsayin dan takarar gwamna a jihar Edo inda Enanulele zai zama mataimakinsa.
- A jam'iyyar AA, Isegjohi Tom mai shekaru 60 da haihuwa ne zai yi takarar gwamnan kuma Onaiwu Mabel Osemwonye Nmwen ne mataimakinsa.
- Jami'yyar AAC ta tsayar da Udo Oberaifo David mai shekaru 37 a matsayin dan takarar gwamna yayin da Osunde Lord Osas zai zama mataimakinsa.
- A bangaren ADC kuma, Izedonmwen Osarenren Derek ne mai 47 zai yi takarar gwamna a Edo sai Osagie Philip mataimakinsa.
- Jam'iyyar ADP ta tsayar da Akhimie Kingson mai shekaru 37 a matsayin dan takarar gwamna sai kuma mataimakiyarsa mai suna Obazee Ramatu
- APC ta tsayar da Okpebholo Monday mai shekaru 53 a matsayin dan takarar gwamna sai kuma Idahosa Dennis a matsayin mataimakinsa.
- APGA ta tsayar da Osifo Isaiah mai shekaru 64 a matsayin dan takara sai Bello Aneru a matsayin mataimaki.
- Jam'iyyar APM ta tsayar da Ugiagbe Odaro Sylvester mai shekaru 45 a matsayin dan takarar gwamna sai Ezomo Timothy Ede a matsayin mataimaki.
- APP ta tsayar da tsayar da Areloegbe Amos Osalumese mai shekaru 56 sai kuma mataimakiyarsa Oyarenua Paul.
- BP ta tsayar da Osiriame Edeipo mai shekaru 47 takarar gwamna a Edo sai kuma mataimakiyarsa mai suna Omorogbe Kingsley.
- LP ta tsayar da Akpata Olumide Anthony mai shekaru 51 takarar gwamnan Edo sai mataimakiyarsa mai suna Alufohai Faith.
- NNPP ta tsayar da Azena Azemhe Friday mai shekaru 44 takarar gwamnan Edo sai mataimakiyarsa Isokpan Ihueghian.
- PDP ta tsayar da Barista Ighodalo Asuerinme mai shekaru 64 takarar gwamnan Edo sai kuma mataimakinsa mai suna Ogie Osarodion.
- Jam'iyyar PRP ta tsayar da Key Patience Ndidi mai shekaru 50 a matsayin yar takara sai mataimakinta Ojo Advice.
- SDP ta tsayar da Anerua Abdulai Aliu mai shekaru 53 a matsayin dan takara sai kuma mataimakinsa Ahmed Paul.
- YPP ta tsayar da Paul Ovbokhan mai shekaru 40 a matsayin dan takara da mataimakinsa Mustapha Ahmed Tijani.
- Jami'yyar ZLP ta tsayar da Akhlamhe Amiemenoghena mai shekaru 43 takarar gwamnan Edo sai mataimakiyarsa mai suna Idubor Joyce Olamilayo.
Atiku ya yi gargadi kan zaben Edo
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira na musamman kan zaben gwamna da ake shirin yi a Edo.
Atiku Abubakar ya ce zaben APC a Edo zai kara mayar da jihar baya kuma hakan na nuni ne da cewa an zaɓi wahala a kan sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng