Damagum: Gwamnonin PDP Sun Fara Kokarin Sauya Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

Damagum: Gwamnonin PDP Sun Fara Kokarin Sauya Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

  • Gwamnonin PDP sun sanar da cewa za su yi koƙarin maido da kujerar shugaban jam'iyyar yankin Arewa ta Tsakiya kamar yadda doka ta tanada
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana hakan bayan ganawa da 'yan NWC
  • Matakin gwamnonin dai ya ci karo da kalaman muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum, wanda ya ce babu wannan dokar a jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce gwamnonin PDP sun fara aiki don tabbatar da kujerar shugaban jam'iyyar na kasa ta koma Arewa ta Tsakiya.

Gwamna Bala, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya ce shi da takwarorinsa sun haɗa kai da ƴan kwamitin gudanarwa (NWC) don cimma wannan burin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da wani shugaban al'umma

Gwamna Bala Mohammed.
Kungiyar gwamnonin PDP sun fara koƙarin maido da kujerar shugaban jam'iyyar yankin Arewa ta Tsakiya Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Twitter

Bala Mohammed ya faɗi haka ne yayin hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan ganawa da tawagar mambobin NWC ranar Talata a Bauchi, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnoni ke son canza shugaban PDP?

Gwamnan ya ce muƙaddashin shugaban PDP na yanzu Umar Damagum ya fito ne daga Arewa maso Gabas, kuma hakan ya saɓawa dokokin jam'iyyar.

A rahoton Leadership, Gwamna Bala ya ce:

"Kundin dokokin PDP ya tanadi cewa duk giɓin da aka samu a shugabancin jam'iyya, dole a cike shi ɗa ɗan yankin wanda ya sauka.
"Arewa ta Tsakiya ta ɗaɗe tana bukatar a dawo mata da matsayin kuma mun tattauna batun, za mu haɗa kai da shugaban NWC da sauran ƴan jami'iyya don ba yankin damar komawa matsayinsa.

Bala ya ƙara da cewa Arewa maso gabas ta ci gajiyar wannan doka bayan Alhaji Bamanga Tukur ya yi murabus lokacin da Ahmadu Muazu daga Bauchi ya zama shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kori kwamishinansa bayan shekara 3, an gano dalilinsa

Gwamnonin PDP sun saɓawa kalaman Damagum

Wannan mataki na gwamnonin PDP na zuwa ne bayan muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum ya ce ba dole ba ne sai ya ci gaba da zama a muƙamin.

A wata hira da ya yi a makon jiya, Damagum ya ce babu wani wuri a kundin tsarin mulkin PDP da ya nuna dole Arewa ta Tsakiya za ta ci gaba da jan ragamar jam'iyyar.

Wike ya gana da ƴan majalisar BoT

A wani rahoton kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya gana da ƴan majalisar amintattu na PDP (BoT) a daren ranar Talata, 17 ga watan Satumba 2024.

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan taro wani wani ɓangare ne a yunƙurin BoT na kawo ƙarshen rigimar siyasar da ta dabaibaye jihar Ribas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262