‘Za Mu Yi Nasara duk da Ana Wahala:’ Jigon APC kan Zabe Mai Zuwa a Edo
- Jigon jami'yyar APC ya ce wahalar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya ba za ta saka yan Najeriya su juwa musu baya ba a Edo
- Tsohon dan majalisa, Ehiozuwa Johnson Agabonayinma ya ce wahalar rayuwa da ake fama da ita ba laifin Bola Tinubu ba ne
- Ɗan siyasar ya ce yan siyasa sun sace biliyoyin kudi a mulkin Muhammadu Buhari wanda hakan na cikin matsalolin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a jam'iyyar APC ya ce tsadar rayuwa ba za ta saka a juwa musu baya a zaben Edo ba.
Ehiozuwa Johnson Agabonayinma ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana kokari duk da matsin tattalin arziki da ake ciki.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ehiozuwa Johnson Agabonayinma ya ce APC ta kammala shirye shirye domin zaben Edo mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wahalar rayuwa da zaben APC a Edo
Tsohon dan majalisar tarayya jihar Edo, Ehiozuwa Johnson Agabonayinma ya ce yana da tabbas a kan yan Najeriya ba za su juya musu baya a zaben gwamna a Edo ba.
Ehiozuwa Johnson ya ce yana da tabbas ne a kan cewa ba shugaban kasa Bola Tinubu ba ne ya jefa kasar cikin wahalar rayuwa a Najeriya.
Bayan haka, ya kara da cewa mutanen jihar Edo sun gaji da mulkin PDP a jihar saboda haka za su so dawowa karkashin APC domin samun cigaba.
An yi sata a mulkin Buhari inji Ehiozuwa
Ehiozuwa Johnson ya ce satar da aka yi a ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari na cikin abubuwan da suka jefa Najeriya a wahalar rayuwa.
Saboda haka ya ce Bola Tinubu ya gaji Najeriya ne bayan an lalata abubuwa a zamanin Buhari wanda shi ma ya samu abubuwa ne a lalace.
A karshe, Ehiozuwa Johnson ya ce dole a tashi tsaye a yaki cin hanci da rashawa idan ana son kawo cigaba mai dorewa a Najeriya.
Edo: An kammala yakin neman zabe
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zaben Edo, an kawo karshen yakin neman zabe da aka yi na tsawon kwanaki a jihar.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban APC, Abdullahi Ganduje sun samu halartar yakin neman zaben inda suka nemi a marawa APC baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng