Zaben Edo: 'Dan Takarar Gwamna Ya Janye, Ya Marawa APC Baya

Zaben Edo: 'Dan Takarar Gwamna Ya Janye, Ya Marawa APC Baya

  • Ɗan takarar gwamnan Edo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar AA ya haƙura da takara a zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
  • Prince Tom Iseghohi-Okojie ya marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo baya a zaɓen gwamnan da ke tafe
  • Ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa Sanata Okpebholo zai kawo shugabanci na gari a jihar ya samu nasarar zama gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar Action Alliance (AA), Prince Tom Iseghohi-Okojie, ya janye daga yin takara a zaɓen.

Prince Tom Iseghohi-Okojie bayan janyewa daga takarar ya marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, baya.

Dan takarar AA ya janye a zaben Edo
Sanata Monday Ekpebholo ya samu goyon baya a zaben Edo Hoto: Senator Monday Ekpebholo
Asali: Facebook

'Dan takarar gwamna ya bi bayan APC a Edo

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Kalamam gwamnan PDP sun tayar da kura ana dab da fara zabe

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Iseghohi-Okojie ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a birnin Benin lokacin da ya koma jam’iyyar APC, tare da ɗimbin magoya bayansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Edo Jarret Tenebe ne ya tarbe su, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Meyasa ya janye daga takarar gwamnan Edo?

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce ko jam’iyyar AA ta haɗe da APC ko ba ta haɗe ba, APC ce za ta lashe zaɓen gwamnan da za a yi ranar Asabar.

Ya ƙara da cewa, shi da magoya bayansa suna son APC ta samu gagarumin rinjaye a zaɓen gwamnan.

Iseghohi-Okojie ya bayyana cewa APC ta hannun Okpebolo za ta iya tabbatar da shugabanci na gari daga ranar 12 ga watan Nuwamba, lokacin da wa’adin Gwamna Godwin Obaseki zai ƙare.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Shugaban PDP ya sha sabon alwashi, ya gargadi INEC

Karanta wasu labaran kan zaɓen Edo

Shugaban PDP ya magantu kan zaɓen Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Illiya Damagum, ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo.

Umar Damagum ya bayyana cewa ƴaƴan jam’iyyar za su yi amfani da jininsu wajen kare ƙuri’unsu a zaɓen gwamnan da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng