PDP da Babban Sifetan Yan Sanda Sun Kai Ruwa Rana kan Zaɓe, IGP Ya Fusata a Bidiyo

PDP da Babban Sifetan Yan Sanda Sun Kai Ruwa Rana kan Zaɓe, IGP Ya Fusata a Bidiyo

  • Sifetan yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya mayar da martani kan zargin cafke wasu mambobin PDP a jihar Edo
  • Egbetokun ya ce ana zargin wadanda aka cafke da kisan dan sanda kuma da kokarin kawo rigima a zaben da za a yi
  • Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar PDP a jihar ta kalubanci Egbetokun kan nuna banbanci a tsakaninta da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Ana cigaba da zargin juna tsakanin jam'iyyar PDP da kuma rundunar yan sandan Najeriya kan zaben jihar Edo.

Babban sifetan yan sanda, Kayode Egbetokun ya zargi bangaren PDP da neman ta da kayar baya a zaben da za a yi.

Kara karanta wannan

Mai garkuwa da mutane ya yanke sassan jikin budurwa bayan karbar kudin fansa

Yan sanda sun yi martani kan cafke mambobin PDP
Babban Sifetan yan sanda ya fadi dalilin cafke mambobin PDP ana daf da zabe. Hoto: @PoliceNG, @GovernorObaseki.
Asali: Twitter

Yan sanda sun magantu kan kama 'yan PDP

Jam'iyyar PDP a jihar, a bangarensa ya zargi Egbetokun da nuna wariya da bangaranci a faifan bidiyo da X-Daily ta wallafa.

Egbetokun ya ce ana zargin mambobin PDP da aka kama da kisan san sanda inda ya ce babu batun nuna bangaranci.

Shugaban yan sandan ya ce wannan ba shi ne karon farko da rundunar ke goyon bayan hukumar INEC ba a zabe, cewar rahoton Vanguard.

"Kuna zargin IGP da nuna bambanci domin ya umarci cafke wasu da zargin kisan dan sanda a filin jirgin sama, idan har wannan a wurinku shi ne wariya to ku cigaba da rike tunaninku har abada."

- Kayode Egbetokun

Obaseki ya ki sanya hannu a yarjejeniya

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Godwin Obaseki ya ki sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben jihar.

Kara karanta wannan

"Za mu hargitsa komai": NLC ta yi barazana kan zaben dan takarar gwamnan PDP a bidiyo

Obaseki ya ba da sharudan cewa sai an sako mambobinsu da aka kama ko kuma a gurfanar da su a Edo madadin Abuja.

NLC ta yi barazana a zaben Edo

Kun ji cewa kungiyar NLC a Edo ta sake rura wutar rikici yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024.

Shugaban kungiyar, Odion Olaye ya nuna ƙarara yana goyon bayan dan takarar gwamna da jam'iyyar PDP ta tsaida, Asue Ighodalo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.