Gwamna Abba Ya Sake Soke Tsarin Ganduje, Ma'aikata Akalla 4,000 Za Su Bar Aiki a Kano

Gwamna Abba Ya Sake Soke Tsarin Ganduje, Ma'aikata Akalla 4,000 Za Su Bar Aiki a Kano

  • Gwamnatin Kano karƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta soke tsarin da ya ƙarawa ma'aikata shekaru biyar a bakin aiki
  • Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya kawo tsarin a lokacin mulkinsa, sai dai Gwamnatin Abba ta koma kan asalin tsarin ritaya
  • Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano, Abdullahi Musa ya ce akalla ma'aikata 4,000 ne za su bar aiki ranar 1 ga watan Disamba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ana tsammanin ma'aikata aƙalla 4,000 da ke aiki ƙarƙashin gwamnatin jihar Kano za su yi ritaya ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

Matakin dai ya biyo bayan soke dokar da ta baiwa ma'aikata damar ci gaba da aiki fiye da shekarun ritaya da kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

N70,000: Gwamna ya yi alkawarin karin albashi, ya kafa sharadi

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano za ta yiwa ma'aikata 4,000 ritaya bayan soke tsarin Ganduje Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Yadda Ganduje ya karawa ma'aikata shekarun aiki

Jaridar Leadership ta tattaro cewa tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya kawo tsarin karawa ma'aikatan shekarun aiki a gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tsarin da Ganduje ya kirkiro, an ƙarawa waɗannan ma'aikata da ake magana a kansu shekaru biyar bayan sun cika shekarun ritaya.

Sai dai a halin yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke wannan tsari na Ganduje, ya maido da asalin tsarin da aka sani a baya.

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kano, Abdullahi Musa shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai bayan soke dokar fansho, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamna Abba ya soke ƙarin wa'adin aiki

Ya ce gwamnati za ta kafa kwamiti na musamman wanda zai zaƙulo dukkan ma'aikatan da wannan matakin ya shafa.

"Kar ku manta a karshen gwamnatin tsohon Gwamna Ganduje ya dauki ma’aikata 13,000 aiki, lokacin da muka zo Gwamna Abba bai kore su ba.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

"Maimakon haka sai muka tantance su, muka ɗauki mutum 10,000 aiki sannan muka sallami sauran. Waɗanda aka kora sun haɗa da matasan NYSC, ɗalibai da ba su gama karatu ba da masu kananun shekaru."
"Da mu ka zurfafa bincike, kwamitinmu ya gano ma'aikata kimanin 4,000 da ake sa ran za su ajiye aiki ranar 1 ga watan Disamba, ma'ana a karshen Satumba za su miƙa takardar shaidar za su yi ritaya."

- Abdullahi Musa.

Za a koma makaranta a Kano

Ku na da labarin gwamnatin jihar Kano ta sanya sabuwar ranar da ɗaliban makarantun firamare da na gaba da firamare za su koma karatu.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilmi ya fitar, ya ce za a koma ne ranakun 15 da 16 ga watan Satumban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262