Gwamnan PDP Ya Kunyata Janar Abdulsalami Ana Neman Sa Hannu a Yarjejeniyar Zabe

Gwamnan PDP Ya Kunyata Janar Abdulsalami Ana Neman Sa Hannu a Yarjejeniyar Zabe

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi fatali da bukatar tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar kan zabe
  • Abdulsalami ya bukaci gwamnan ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin zaben gwamnan da za a yi a Edo
  • Sai dai gwamnan ya ce ba zai sanya hannu a yarjejeniyar ba saboda babu alamun zaman lafiya bayan cafke 'yan PDP 60

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya ki amincewa da sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben jihar Edo.

Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar shi ne ya jagoranci zaman inda ya fadawa Obaseki muhimmancin haka.

Gwamnan PDP ya yi fatali da bukatar Abdulsalami Abubakar kan zabe
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya. Hoto: Godwin Obaseki, Abdulsalami Abubakar.
Asali: Facebook

Gwamna ya yi fatali da yarjejeniyar zaman lafiya

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur ya tilastawa Gwamna karawa ma'aikata hutu a kowane mako

Gwamnan ya ki amincewa da yarjejeniyar ce a cikin wani bidiyo da @Tony_Ogbuagu ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obaseki ya ce ba zai sanya hannu ba har sai yan PDP da aka kama an sake su ko kuma gurfanar da su kan laifinsu.

Ya koka kan yadda babban sifetan yan sanda ya umarci kama mambobin PDP 60 ba bisa ka'ida ba a jihar.

Har ila yau ya ce ya kamata a gurfanar da su a jihar Edo amma aka wuce da su Abuja ba tare da yin wani abu ba.

Abdulsalami ya fadi muhimmancin yarjejeniyar zaman lafiya

Tun farko, Abdulsalam Abubakar ya fadawa gwamnan muhimmancin yarjejeniyar game da zaben da za a yi.

Abdulsalami ya ce hakan zai taimaka musamman ganin yadda zaben ke tafe saboda gudun a samu matsaloli yayin gudanar da zaben kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki, ya faɗi kuɗin da Tinubu ya turo

'Dan takarar APC ya kwafsa yayin kamfe

Kun ji cewa an yi ta ce-ce-ku-ce bayan kuskuren da dan takarar gwamnan APC a jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi yayin kamfe.

An gudanar da kamfe din ne a karamar hukumar Ovia ta Arewa da ke jihar inda Okpebholo ya tafka kuskure lokacin jawabi ga al'umma.

Yayin kamfen, Okpebholo ya yi wa yan jihar alkawarin zai kawo musu 'rashin tsaro' wanda kowa ya sha mamaki a lokacin da ya ya yi maganar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.