Sakataren Gwamnatin Jiha Ya Yi Murabus, Gwamna Ya Naɗa Mace Nan Take

Sakataren Gwamnatin Jiha Ya Yi Murabus, Gwamna Ya Naɗa Mace Nan Take

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya naɗa Barista Aber Deborah a matsayin sabuwar sakatariyar gwamnatin jiha (SSG)
  • Alia ya yi wannan sanaɗi ne bayan Farfesa Joseph Alakali ya yi murabus daga kujerar SSG saboda wasu dalilai na ƙashin kansa
  • Gwamnan ya amince da murabus din tare da naɗa mace a matsayin da za ta maye gurbinsa a yau Talata, 10 ga watan Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya nada Misis Deborah Aber a matsayin sabuwar sakatariyar gwamnatin jihar (SSG).

Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Farfesa Joseph Alakali ya mika takardar murabus daga matsayin sakataren gwamnati ga Gwamna Alia ranar Litinin.

Kara karanta wannan

"Abu 1 muke jira," Gwamna ya faɗi abin da ya hana shi fara biyan albashin N70,000

Gwamna Hycinth Alia.
Gwamna Alia ya nada sabuwar sakatariyar gwamnatin jihar Benue Hoto: Fr. Hycinth Lormem Alia
Asali: Facebook

Gwamna Alia ya maye gurbin SSG

Gwamna Alia ya amince da murabus ɗin tsohon SSG tare da naɗa Misita Deborah a matsayin wacce za ta maye gurbinsa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren watsa labaran gwamnan Benuwai, Tersoo Kula, shi ne ya bayyana sabon naɗin a wata sanarwa da ya fitar a Makurɗi.

Sanarwar ta ƙara da cewa naɗin Misis Deborah zai fara aiki ne nan take daga yau Taata, 10 ga watan Satumba, 2024.

Dalilin tsohon sakataren gwamnati na yin murabus

Wani sashen sanarwar ya ce:

"Gwamna Hyacinth Alia ya amince da nadin Barista Aber Serumun Deborah a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar SSG. Nadin ya biyo bayan murabus din tsohon SSG, Farfesa Joseph Alakali.
“Alkali ya mika wasikar murabus dinsa a jiya, inda ya bayyana cewa yana bukatar lokaci don magance kalubalen da ke gabansa.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Sanata Ndume ya nuna alhininsa, ya ba gwamnati shawara

"Gwamna Alia ya karɓi murabus din kana ya jinjinawa Farfesa Alakali bisa yadda ya yiwa jihar hidima a gwamnatinsa na tsawon shekara daya da watanni uku."

Mace ta zama SSG a Benue

Sabuwar sakariyar da gwamnan ya naɗa ta yi karatunta ne a Jami’ar Jos da Jami’ar Jihar Nasarawa, rahoton AIT.

Gwamna Alia ya bayyana yaƙinin cewa duba da gogewarta a fagen aiki, yana fstan sabuwar sakariyar za ta ƙara ɗaga darajar gwamnatinsa wajen yiwa mutane hidima.

Gwamna Alia ya tsokano Ortom

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom kam zargin kin biyan haraji na makudan kudi.

Ana zargin kamfanin mai suna Oracle Business mallakin tsohon gwamna, Ortom da kin biyan haraji har N93.5m.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262