Peter Obi: DSS Sun Cafke Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a 2023? Hadiminsa Ya Yi Magana

Peter Obi: DSS Sun Cafke Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a 2023? Hadiminsa Ya Yi Magana

  • Mai taimakawa Peter Obi kan harkokin yada labarai ya musanta raɗe-raɗin kama tsohon gwamnan kuma jigon LP a gidansa a Anambra
  • Val Obienyem ya bayyana rahoton da ke yawo cewa DSS ta kama Obi a matsayin ƙarya mara tushe, ya roki ƴan Najeriya su yi watsi da ita
  • Ya kuma musanta wata jita-jitar cewa an kama matar Peter Obi, inda ya ce masu shirya ƙaryar suna da wata mummunar manufa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Mista Peter Obi ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa jami'an DSS sun cafke tsohon gwamnan.

Wasu rahotanni dai sun yi iƙirarin cewa jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun yi ram da Peter Obi a gidansa da ke Anambra.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari da asuba, sun kashe bayin Allah a Arewa

Peter Obi.
Hadimin Peter Obi ya musanta kama tsohon gwamnan a Anambra Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: UGC

Sai dai mai magana da yawun Obi, Mr. Val Obienyem ya ƙaryata jita-jitar a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 10 ga watan Satumba, 2024, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske DSS ta kama Peter Obi?

Mista Obienyem ya yi watsi da zargin kama Obi, inda ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya mara tushe balle makama.

Ya ce jita-jitar ta fara fitowa ne ranar Asabar amma aka yi gaggawar watsi da ita, daga bisani kuma ta ci gaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta.

A cewar Obienyem, Mista Obi ba ya cikin jihar Anambra a lokacin da ake zargin dakarun DSS sun kama shi.

Ya ce:

"A ranar Asabar din da ake magana Peter Obi yana ƙasar Ruwanda, yanzu kuma ya dawo Najeriya ya wuce jihar Edo domin halartar wasu harkokin jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

APC ta faɗi gwamnan da take zargin yana shirya gagarumar zanga zanga a Najeriya

"Jami'an DSS ba su je gidansa ba balle kuma a fara zancen wai sun kama shi, labarin ba gaskiya ba ne."

DSS ta cafke matar Peter Obi?

Obienyem ya kuma musanta raɗe-taɗin cewa an kama matar Obi, ya bayyana labarin da ƙage wanda aka shirya da nufin tunzura magoya bayansa.

Ya bukaci al'umma da su yi watsi da wannan karyar, su kuma yi taka tsan-tsan kan yada labaran karya, Daily Trust ta rahoto.

APC ta zargi Obaseki da shirya zanga-zanga

A wani rahoton na daban APC ta zargi gwamnan Edo, Godwin Obaseki da shirya zanga-zanga domin kawo cikas a zaɓen jihar da Najeriya baki ɗaya.

Kwamitin kamfen APC ya ce gwamnan ya haɗa baki da wasu jihohin da PDP ke mulki domin fara zanga-zanga ranar 15 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262