Gwamna Ya Kori Hadiminsa daga Aiki kan Wani Bidiyo da Ya Fitar? Bayanai Sun Fito
- Gwamnan jihar Anambra ya musanta raɗe-raɗin tsige hadiminsa kan bidiyon da aka saki yana tika rawa a soshiyal midiya
- Farfesa Charles Soludo ya bayyana jita-jitar a matsayin ƙarya mara tushe, inda ya tabbatar da cewa babu wanda ya kora daga aiki
- Mai magana da yawun gwamnan ya ce wanda ake zargin gwamnan ya kora sauya masa wurin aiki aka yi ba tsige shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya musanta korar ɗaya daga cikin hadimansa kan bidiyon gasar rawar 'gwo gwo ngwo’.
Gwamma Suludo ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Christian Aburime ya fitar ranar Litinin.
Ana zargin gwamnan ya kori hadiminsa
Punch ta gano cewa jim kadan bayan faifan bidiyon ya yadu, gwamnatin jihar ta sanar da nadin Mista Christopher Molokwu, a matsayin shugaban kafar watsa labaran Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Molokwu ya maye gurbin Mr Chido Obidiegwu wanda gwamnatin Anambra ta yi gum ba ta bayyana dalilin saukarsa daga muƙamin ba.
Hakan ya haddasa ka-ce-na-ce tsakanin al'umma inda wasu suka fara yaɗa cewa cire Obidiegwu na da alaƙa da wannan bidiyon da aka ga gwamna na tiƙa rawa.
Da gaske gwamna ya sallami hadiminsa?
Sai dai kakakin gwamnan, Christian Aburime ya musanta hakan, yana mai cewa canza masa wurin aiki aka yi ba wai korarsa Soludo ya yi ba.
Mai magana da yawun gwamnan ya ce:
"An jawo hankalin gwamnatin Anambra kan wasu labaran ƙarya da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa Gwamna Soludo ya kori hadiminsa wanda ya saki bidiyon gwamnan yana tiƙa rawa."
"Muna tabbatarwa al'umma cewa labarin karya ne kuma ba shi da tushe, babu wanda gwamna ya kora kan bidiyon da aka saki na gasar rawar gwo gwo ngwo."
"Wanda ake yaɗa gwamnan ya sallama daga aiki canza masa wurin aiki aka yi a wani ɓangaren na sauye-sauyen gwamnati na yau da kullum."
APC ta janye daga zaɓen Anambra
A wani rahoton kuma jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar ba.
APC ta bayyana cewa za ta shigar da ƙara a gaban kotu idan har hukumar zaɓen jihar ta gudanar da zaɓen kamar yadda ta tsara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng