“Babu Wanda Ya Tsira”: Miyagu Sun Fasa Ofishin Gwamnan APC, Sun Yashe Kaya

“Babu Wanda Ya Tsira”: Miyagu Sun Fasa Ofishin Gwamnan APC, Sun Yashe Kaya

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo, wasu miyagu sun balla ofishin kamfe na Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  • Miyagun sun yi amfani da daukewar kafa da dare inda suka yi nasarar fasa ofishin kamfe na LACO-FSIC tare da satar kayayyaki
  • Rahotannin sun tabbatar da cewa bayan satar kayan da gan-gan aka lalata wasu kaya da ake ganin akwai siyasa a cikin lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Yan daba sun balla ofishin kamfe na Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo.

Miyagun sun fasa ofishin kamfen Gwamna Lucky inda suka yashe duka kayayyakin da ke ciki.

Yan daba sun fasa ofishin kamfen gwamnan APC ana daf da zab
Wasu miyagu sun balla ofishin kamfen Gwamna Aiyedatiwa na Ondo ana daf da zaben jihar. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Twitter

Miyagu sun shiga ofishin kamfen gwamnan Ondo

Kara karanta wannan

2027: Shekarau zai jagoranci tawaga mai karfi domin kifar da Tinubu, sun fara shiri

Tribune ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yada labaran kungiyar LACO-FSIC, Kayode Fasua shi ya tabbatar da haka inda ya ce akwai zargin bita-da-kullin siyasa.

Fasua ya ce kungiyarsu ta yi Allah wadai da harin inda ta ce miyagun bayan satar kaya sun lalata abubuwa da dama.

Ana zargin yan adawa da kisa harin

"Duba da yadda aka yi barnar, hakan ya tabbatar da cewa yan adawa ne suka shirya duk da kokarin Gwamna Aiyedatiwa na neman zaman lafiya da su."
"Yadda aka yi amfani da dabara wurin balla ofishin da kuma satar kayan da aka yi ya tabbatar da hannun wasu wanda abin ya ba kowa mamaki>"

- Kayode Fasua

Fasua ya ce akwai alamun yan adawa sun turo yan saka ido wurin ganawar da suka wanda hakan ya tayar musu da hankali saboda ganin yadda suka shirya.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina, ta shafi bangaren ofishin gwamna

Ondo: 'Yan APC da dama sun gudu

A wani labarin, kun ji cewa magoya bayan jam'iyyar APC da dama ne suka watsar da kashinta a jihar Ondo.

Daruruwan mambobin APC sun sauya sheka ne zuwa jam'iyyar SDP ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar.

Darakta-Janar na kamfen jam'iyyar, Femi Ikoyi ya karbi sababbin tuban a birnin Akure a ranar Talata 27 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.