Gwamna Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Jam'iyya Ta Fara Shirin Ɗaukar Mataki a Kansa

Gwamna Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Jam'iyya Ta Fara Shirin Ɗaukar Mataki a Kansa

  • Jam'iyyar APGA ta fara shirin ɗaukar matakin ladabtarwa kan gwamna ɗaya tilo ɗa take da shi a Najeriya, Charles C. Soludo
  • Shugaban BoT na APGA, Dr. Chekwas Okorie ya ce babu wanda ya fi ƙarfin a hukunta shi matukar ya aikata laifi a jam'iyyar
  • Ya kuma roki kwamitin NWC na ƙasa ya gudanar da bincike domin ɗaukar mataki kan masu cin amana da yi masu zagon ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - All Progressives Grand Alliance (APGA) za ta hukunta gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo bisa zargin cin amanar jam'iyyar.

Shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar APGA ta ƙasa, Dr. Chekwas Okorie ne bayyana hakan ranar Lataba, 4 ga watan Satumba, 2024 a Abuja.

Kara karanta wannan

Nenadi Usman: An naɗa mace a matsayin shugabar jam'iyya ta ƙasa a Najeriya

Gwamna Soludo.
Jam'iyyar APGA na shirin hukunta Gwamna Soludo na jihar Anambra Hoto: Charles Chikwuma Soludo
Asali: Facebook

Meyasa APGA za ta hukunta Soludo?

Vanguard ta tattaro cewa APGA na shirin ladabtar da gwamnan sakamakon rashin mutunta hukuncin kotun koli kan rigimar shugabancin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun koli ta yanke hukuncin tabbatar da Edozie Njoku a matsayin sahihin shugaban APGA na ƙasa, lamarin da ake zargin bai yiwa Gwamna Soludo daɗi ba.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba, Okorie ya bayyana cewa ayyukan Soludo na ƙara lalata muradu da kimar APGA.

A cewarsa, wannan dalili ne ya sa jam'iyyar APGA ta shirya ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda ta gano yana da hannu a yi mata zagon ƙasa ko cin amana.

APGA ta yi koƙarin lallaɓa Soludo

Shugaban BoT ya ƙara da cewa APGA ta sha yi wa Gwamma Soludo tayin sasanci domin a zauna lafiya, amma abin mamakin ya fatali da tayin, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban kasa ya shiga taron NEC da manyan attajirai 2, bayanai sun fito

"APGA za ta zaƙulo koma wanene har da Farfesa Charles Soludo, babu wanda ya fi ƙarfin ladabtarwa, ba za mu bari wani ya ɗaƙile yunƙurin jam'iyya na dawo da ƙimarta a siyasar Najeriya ba.
"Ina shawartar kwamitin gudanarwa (NWC) ya ɗauki matakin ladabtarwa kan duk wanda aka gano yana yiwa jam'iyyar APGA zagon ƙasa."

-Dr. Chekwas Okorie.

Gwamma Soludo ya magantu kan albashin ƴan siyasa

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Anambara ya fadi kudin da ya kamata gwamnati ta rika biyan yan siyasa albashi a kowane wata.

Gwamna Charles Soludo ya fadi haka ne yayin da takaddama ta ƙi karewa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262