Ganduje: Tinubu, Buhari da Wasu Kusoshi Za Su Yanke Makomar Shugaban APC

Ganduje: Tinubu, Buhari da Wasu Kusoshi Za Su Yanke Makomar Shugaban APC

  • Ana ci gaba da muhawara kan kujerar shugaban APC na ƙasa wanda tsohon gwamnan Kano yake kai a yanzu haka
  • Wannan ya sa ake sa ran taron NEC na APC da za a yi a watan Satumba zai tattauna kan batun kuma ya yanke hukunci
  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinsa,Yemi Osinbajo na cikin waɗanda ake sa ran za su je taron NEC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Batun kujerar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa na cikin manyan batutuwan da ake sa ran taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) zai tattauna a kai.

A ranar 11 da 12 ga watan Satumba, 2024, za a gudanar da taron NEC, majalisar ƙoli mai alhakin zartar da hukunci kan harkokin ciki gida a jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Kebbi: APC ta mayar da martani bayan sanar da sakamakon zaben ƙananan hukumomi

Bola Tinubu, Buhari da Ganduje.
Da yiwuwar za a warware taƙaddama kan kujerar shugaban APC Ganduje a taron NEC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

The Guardian ta tattaro cewa kujerar shugabancin APC da Abdullahi Umar Ganduje yake kai yanzu haka na ci gaba da haddasa muhawara tsakanin ƴaƴan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake musayar yawu kan kujerar Ganduje

A ƴan kwanakin nan, jiga-jigan APC sun yi musayar yawu kan makomar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyya na ƙasa.

Lamarin ya fara ne lokacin da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya jaddada goyon bayansa ga Ganduje da sauran ƴan kwamitin gudanarwa na NWC.

Sule, shugaban gwamnonin APC a Arewa ta Tsakiya ya buƙaci ƴaƴan jam'iyyar su marawa Ganduje baya musamman saboda zaɓen Edo da Ondo da ake tunkara.

Sai dai shugaban ƙungiyar mambobin APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga, ya yi fatali da kalaman Gwamna Sule, inda ya ce hakan rashin adalci ne.

A cewarsa, kujerar shugaban APC ta yankinsu ce, yana mai cewa Gwamna Sule ya ci amanar jihar Nasarawa da Arewa ta Tsakiya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shiga matsala: An gano shirin Atiku, Obi, Kwankwaso na hade kansu a 2027

Da yake martani, Cif Oliver Okpala ya nanata cewa kalaman Gwamna Sule kan Ganduje suna kan hanya kuma duk wani ɗan APC mai kishi da tunani matsayarsa kenan.

NEC za ta raba gardama kan kujerar Ganduje

Sakataren APC na ƙasa, Dr Surajuddeen Ajibola ya tabbatar da za cewa za gudanar da taron NEC a rankun 11 da 12 ga watan Satumba, 2024.

Waɗanda ake sa ran za su halarta sun haɗa da Shugaba Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo da sauran ƙusoshin APC.

Ganduje na shirin kwace jihohin Najeriya

A wani rahoton kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar na shirin ganin jihohin Najeriya 36 sun dawo hannunta.

Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓukan gwamna a jihar Ondo da Edo waɗanda za a yi a wannan shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262