Kebbi: APC Ta Mayar da Martani bayan Sanar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi
- Jam'iyyar APC mai mulki ta samu nasarar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a jihar Kebbi
- A ranar Asabar, 31 ga watan Agusta aka gudanar da zaɓen kananan hukumomi wanda PDP ta tsame kanta bisa zargin maguɗi
- Jam'iyyar APC mai mulki ta ce zaɓen ya gudana cikin lumana babu tashin hankali kuma al'umma sun ba da haɗin kai wajen zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - All Progressives Congress (APC) ta lashe zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kebbi ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban hukumar zaɓen jihar Kebbi mai zaman kanta, Hon Aliyu Muhammed Mera shi ne ya sanar da sakamakon a Birnin Kebbi.
Ya ce jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkan kujerun ciyamomi da mataimakansu da kuma kansiloli, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta faɗi yadda zaben ya gudana
Sai dai a wata sanarwa da kakakin APC, Isah Abubakar Assalafi ya fitar, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana a dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar.
Ya ce al'umma sun ba da haɗin kai, sun fito rumfunan zaɓensu kuma sun jefa ƙuri'a ba tare da fuskantar wata tangarɗa ba.
Jam'iyyar APC ta musanta iƙirarin PDP
Isah Assalafi ya kuma yi watsi da ikirarin jam'iyyar PDP cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ya ce an tura jami'an tsaro kowane akwati, cibiyoyi da ofisoshin hukumar zaɓe.
Kakakin APC ya bayyana cewa kwararru sun sa ido kan yadda aka gudanar da zaɓen, wanda hakan alama ce da ke nuna an yi sahihi kuma ingantaccen zaɓe.
Ya yaba da yadda mutane suka fito suka kaɗa kuri'unsu cikin lumana babu fargaba ko ta da yamutsi, kamar yadda PM News ya kawo a rahotonta.
Atiku na da damar tsayawa takara a 2027?
A wani rahoton kuma wani jigo a PDP, Glintstone Akinniyi ya yi bayanin yadda Atiku Abubakar zai iya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Akinniyi ya ce idan Atiku na son takara ya zama tilas ya fito ya nema, inda ya ƙara da cewa jam'iyyu ba su ba mutum takara sai ya nema.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng