'Yadda Atiku Abubakar Zai Zama Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na Jama'iyyar PDP a 2027'

'Yadda Atiku Abubakar Zai Zama Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na Jama'iyyar PDP a 2027'

  • Wani jigo a PDP, Glintstone Akinniyi ya yi bayanin yadda Atiku Abubakar zai iya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Akinniyi ya ce idan Atiku na son takara ya zama tilas ya fito ya nema, inda ya ƙara da cewa jam'iyyu ba su ba mutum takara sai ya nema
  • A wata hira da Legit.ng ranar Asabar, 31 ga watan Agusta, 2024, Mista Akinniyi ya soki shirin PDP na ware tikitin takarar shugaban ƙasa ga wani yanki kaɗai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kakakin ƙungiyar matasan PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa ka iya samun tikitin takara na jam'iyyar a 2027.

A cewarsa, haka kurum Atiku ba zai samu tikitin takara ba har sai ya fito ya gwabza da ƴan takara sannan ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Malami ya bayyana hanya 1 da za a iya kayar da Shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Atiku Abubakar.
Jigon PDP ya bayyana yadda Atiku zai iya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Yadda PDP za ta tsaida ɗan takara

Jigon PDP ya nanata cewa babu wata jam'iyyar siyasa wadda ta san abin da take yi da za ta ɗauki tikitin takarar ta ba mutum haka kurum ba tare da ya nema ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Akinniyi ya jaddada cewa dole PDP ta amince duk mai sha'awar takara ya fito a fafata wanda Allah ya ba nasara ya zama ɗan takara.

Wannan kalamai na nasa na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban PDP, Bode George ya buƙaci Atiku ya jira 2031 idan yana son sake neman takara.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, George ya ce tun da Muhammadu Buhari, ɗan Arewa ya gama shekaru takwas, ya kamata a bar Kudu ta yi shekara takwas a mulki.

Atiku na da damar tsayawa takara

A wata hira da Legit Hausa, Akinniyi ya ce har yanzu Wazirin Adamawa na da damar zama ɗan takarar shugaban ƙasa idan har ya amince ya fito takara.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin jam'iyyar APC ya tarewa Atiku Abubakar faɗa kan takara a 2027

“Babu wata jam’iyyar siyasa da haka kurum za ta ware mutum ta ba shi ‘tikitin’ na shugaban kasa, dole ne sai an fafafa. Idan PDP ya yanke miƙa takarar ga wani yanki, za mu yi ɗa'a.
"Amma taya za ku killace tikiti a yaki guda bayan kuna tsagin adawa? Atiku ya cancanta ya shiga takara idan yana sha'awar sake neman zama shugaban ƙasa."

Atiku ya gaisa da Nuhu Ribadu a Masallaci

A wani rahoton kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya haɗu da Nuhu Ribadu a wurin sallar Jumu'a tare da sauran Musulmi a Abuja

Atiku dai babban jagoran adawa ne a Najeriya yayin da Nuhu Ribadu ke aiki tare da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai bada shawara kan tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262