Babbar Kotu Ta Ƙara Jiƙawa Ganduje Aiki kan Korar Wasu Shugabannin APC

Babbar Kotu Ta Ƙara Jiƙawa Ganduje Aiki kan Korar Wasu Shugabannin APC

  • Wata babbar kotun jiha mai zama a Makurɗi ta tsawaita umarnin wucin gadin da ta bayar na hana tsige shugabannin APC a Benuwai
  • Wannan dai na zuwa ne bayan APC ta ƙasa ta kori shugabannin jam'iyyar na jihar Benuwai tare da naɗa kwamitin rikon ƙwarya
  • APC dai na fama da rigingimun cikin gida a jihar musamman tsakanin magoya bayan George Akume da Gwamna Hyacinth Alia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Babbar kotun jihar Benuwai ta tsawaita wa'adin umarnin wucin gadi na hana jam'iyyar APC rusa kwamitin gudanarwa na jihar karkashin Austin Agada.

Rikicin cikin gida dai ya dabaibaye APC reshen Benue wanda ya kai ga rabewar jam'iyyar zuwa gida biyu.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Rikicin APC a Benue.
Benue: Kotu ta tsawaita umarnin hana rushe shugabannin APC Hoto: @OfficialAPC
Asali: Twitter

Daily Trust ta ce tsagi ɗaya na goyon bayan Gwamna Hyacinth Alia yayin da ɗayan tsagin ke tare da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya rusa shugabannin APC na Benue

Sakamakon haka ne kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa karƙashin shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kori dukkan masu ikirarin shugabancin jam'iyya a Benuwai.

Kazalika jam'iyyar APC ta ƙasa ta naɗa kwamitin rikon kwarya wanda ya ƙunshi magoya bayan Akume da Gwmana Alia, duk a yunkurin kawo karshen rikicin.

Sai dai bangaren da ke karkashin Agada ya samu umarnin kotu a ranar 21 ga watan Agusta, inda alƙali ya hana rusa kwamitinsa, umarnin da APC ta kasa ta yi watsi da shi.

Yadda zaman kotun ya kasance

A zaman ci gaba da sauraron shari'ar rananr Laraba, lauyan tsagin Agada, M.T. Alyebo, Esq ya buƙaci kotun ta tsawaita umarnin da ta bayar a baya.

Kara karanta wannan

Rikici na neman ruguza APC a jihar Arewa, jam'iyya ta kira taron gaggawa

Lauyan APC ta ƙasa, Yahaya D. Dangana da lauyoyi bakwai ciki har da Antoni Janar na jihar sun shaidawa kotu cewa jam'iyyar tana da ikon rushe kowane kwamitinta.

Benue: Kotu ta tsawaita wa'adin hana tsige Agada

Bayan haka ne mai shari'a Theresa Igoche ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin umarnin wucin gadin da kwanaki bakwai, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Alkalin ta kuma yi watsi da ikirarin lauyan APC cewa kotu ta ba da wannan umarni ne bayan jam'iyyar ta riga ta kori shugabannin tsagin Agada.

APC ta yiwa Moghalu bankwana

A wani rahoton jam'iyyar APC ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta ji mamaki ba da George Moghalu ya ɗauki matakin barin jam'iyyar bayan tsawon lokaci.

Moghalu na ɗaya daga cikin iyayen APC da suka haɗu suka kafa ta, sai dai ya sanar da ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262