"Ba Mu Yi Mamaki ba," Jam'iyyar APC Ta Yi Magana kan Ficewar Babban Jigonta

"Ba Mu Yi Mamaki ba," Jam'iyyar APC Ta Yi Magana kan Ficewar Babban Jigonta

  • APC ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta ji mamaki ba da George Moghalu ya ɗauki matakin barin jam'iyyar bayan tsawon lokaci ba
  • Moghalu na ɗaya daga cikin iyayen APC da suka haɗu suka kafa ta, sai dai ya sanar da ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai
  • Mataimakin sakataren tsare-tsaren APC ta ƙasa, Nze Duru ya ce dama tuni Moghalu ya fara nuna alamun zai kama gabansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC, Dr. George Moghalu ya fice daga jam'iyyar.

Yayin da take mayar da martani, jam'iyyar APC ta kasa ta ce ko kaɗan ba ta yi mamakin ficewar Moghalu ba domin ta fahimci shirinsa tuntuni.

Kara karanta wannan

Ganduje ya tafka asara, daruruwan 'yan APC sun watsar da ita ana daf da zabe

George Moghalu.
APC ta ce ba ta yi mamakin ficewa George Moghalu daga cikinta ba Hoto: George Moghalu
Asali: Twitter

APC ta maida martani kan ficewar Moghalu

Mataimakin babban sakataren tsare-tsaren jam’iyyar APC na kasa, Nze Duru, ya shaida wa wakilin Punch cewa wasikar ficewar Moghalu duk shiri ne kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Duru ya ce:

"Moghalu ya daɗe da barin APC, ya riga ya tsara komai, tun tuni ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar. Muna masa fatan alheri a duk inda ya tsinci kansa."
"Yana daga cikin mutanen da suka amfana da APC sosai to amma bisa wani dalili da shi kaɗai ya sani, ya ɗauki matakin barin jam'iyyar, muna masa fatan alheri.

Ana kyautata zaton dai Moghalu na da burin tsayawa takarar gwamnan jihar Anambra a zaben da za a yi a shekarar 2025.

Anambra: APC ta aika saƙo ga Moghalu

Mataimakin sakataren yada labarai na APC reshen jihar Anambra, Hilary Ogemdi, ya ce jam’iyyar ba ta da cikakken bayanin dalilin ficewar Moghalu har yanzu.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Ogemdi ya ce:

"A soshiyal midiya muka ga labarin Moghalu ya fita daga APC, har yanzun ba a sanar da jam'iyyar reshen Anambra a hukumance ba.
"Muna masa fatan alheri a duk abin da ya sa a gaba amma kafin ya ɗauki wannan matakin, mun san yana da burin neman takarar gwamnan Anambra a inuwar APC."

Jigon PDP ya buƙaci Atiku ya jira 2031

A wani rahoton kuma Bode George ya bayyana cewa Atiku Abubakar ba zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027 ba sai dai ya jira 2031.

Tsohon shugaban na PDP ya ce a hankalce da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyyarsu, mulki zai ci gaba da zama a kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262