Peter Obi Ya Hada Kai da Gwamna, Sun Shirya Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki a LP

Peter Obi Ya Hada Kai da Gwamna, Sun Shirya Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki a LP

  • Mista Peter Obi da Gwamna Alex Otti sun kira taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar LP karo na farko bayan zaɓen 2023
  • Mai magana da yawun gwamnan Abia, ya ce za a gudanar da taron ranar 4 ga Satumba, 2024 a gidan gwamnati da ke Umuahia
  • Ana sa ran manyan kusoshin Labour Party da suka haɗa da Obi, Gwamna Otti, sanatoci da ƴan majalisar wakilai su halarci taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Ɗan takarar shugaban kasa na LP a zaɓen 2023, Peter Obi da Gwamna Alex Otti na jihar Abia sun kira taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar.

Manyan ƙusoshin Labour Party sun sanar da cewa taron zai gudana a rana 4 ga watan Satumba, 2024 a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Abia.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Gwamna Otti da Peter Obi.
Jam'iyyar LP ta kira taron masu zuwa da tsaki na ƙasa Hoto: Alex C Otti
Asali: Facebook

Mai magana da yawun Gwamna Alex Otti na Abia, Dodoh Okafor ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda The Nation ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene maƙasudin shirya taron LP?

Mista Okafor ya bayyana cewa an kira wannan taron ne domin ƙara gina jam'iyar LP, ta sake farfaɗowa a fagen siyasar Najeriya.

A cewar sanarwar taron, masu ruwa da tsaki a taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, Gwamna Alex Otti, da tsohon abokin takarar Obi, Datti Baba-Ahmed.

Sauran sun ƙunshi shugabannin LP karkashin jagorancin Julius Abure, sanatocin jam'iyyar da ƴan majalisar wakilan tarayya da dai sauransu.

Manyan ƙusoshin LP za su hallara a Abia

Sanarwar ta ƙara da cewa ana tsammanin wakilan ƴan takarar gwamna daga dukkan shiyyoyi shida na Najeriya zasu halarci wannna taro.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribaɗu ya yi babban rashi, Allah ya yiwa surukarsa rasuwa a Abuja

Taron kamar yadda sanarwar ta ambata zai maida hankali ne wajen duba hanyoyin da za a kara gina jam'iyyar LP da nazari kan abubuwan da ke faruwa.

Wannan zama dai na masu ruwa da tsakin LP na zuwa a lokacin da ƴan siyasa musamman a jam'iyyun adawa suka fara shirin tunkarar zaɓen 2027.

Ambaliya ta ci gidaje a Kaduna

A wani rahoton kuma mummunar ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a ƙananan hukumomin Zaria da Sabon Gari da ke jihar Kaduna.

Shugaban hukumar bada agaji a Kaduna, Dr. Usman Hayatu Mazadu ya ce gwamnati ta ɗauki matakai amma mutane suka yi kunnen ƙashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262