“Zan Tsaya da Kafafuna”: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sha Alwashi, Ya Bugi Kirji

“Zan Tsaya da Kafafuna”: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sha Alwashi, Ya Bugi Kirji

  • Yayin da ake zargin juya wasu masu rike da madafun iko, Dan takarar gwamnan PDP a jihar Edo ya sha alwashi
  • Asue Ighodalo ya sha alwashin tabbatar da ya tsaya da kafafunsa ba tare da barin wasu suna juya shi kamar waina ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan Edo a watan Satumbar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Dan takarar gwamnan jihar Edo a PDP, Asue Ighodalo ya ce ba zai taba bari a cigaba da juya shi ba idan ya ci zaben gwamnan jihar.

Ighodalo ya bugi kirji inda ya ce zai tabbatar ya kasance mai yanke hukunci ko daukar matakai a karan kansa.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Dan takarar PDP ya ce ba zai bari a juya shi ba a mulki
Dan takarar gwamnan Edo a PDP, Asue Ighodalo ya ce babu mai juya shi idan ya hau mulkin jihar. Hoto: Asue Ighodalo.
Asali: Facebook

Edo: Dan takarar PDP ya sha alwashi

Dan takarar gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels TV a jiya Litinin 26 ga watan Agustan 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ighodalo ya ce zai yi kokarin kaucewa duk wasu masu neman juya akalarsa tare da yin taka tsan-tsan wurin gudanar da mulkinsa.

Ya ce tun yana shekaru 18 ya ke kula da kansa ba tare da an juya shi ba inda ya ce hakan zai taimaka wurin samar da shugabanci nagari, cewar TheCable.

Ighodalo ya tsara yadda zai yi mulkinsa

"Tabbas zan tsaya da kafafuna, na dade ina kula da kaina tun ina shekaru 18 a duniya."
"Iyayena sun yi mani tarbiya domin daukar mataki ko yanke hukunci da kai na, na yi abubuwa da dama a rayuwa ta."
"Amma wannan ba shi yake nufin ba zan dauki shawarwari daga mutane ba musamman da suke da kwarewa a wannan bangaren."

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

- Asue Ighodalo

Yan bindiga na farautar dan takarar gwamna

A wani labarin, kun ji cewa ana shirin zaben gwamnan Edo a watan Satumba dan takarar AAC, Udoh Oberaifo ya ce an yi yunkurin yin garkuwa da shi.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Benin, Udoh ya kuma yi zargin cewa an lalata allunan yakin neman zabensa a birnin da ke jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.