Kotun Koli Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci kan Sahihancin Nasarar Gwamnan PDP

Kotun Koli Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci kan Sahihancin Nasarar Gwamnan PDP

  • Kotun ƙoli ta kori ƙarar tsohon ƙaramin ministan fetur, Timipre Sylva kana ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri a zaɓen Bayelsa
  • A zaman yanke hukunci ranar Jumu'a, 23 ga watan Agusta, kwamitin alkalai biyar na kotun ya kori karar Sylva bisa rashin cancanta
  • Gwamna Diri ya samu nasarar doke babban abokin karawarsa na APC a zaben an jihar Bayelsa da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa a zaɓen da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta kori ƙarar da tsohon ƙaramin ministan man fetur, Timipre Sylva ya ɗaukaka zuwa gabanta yana ƙalubalantar nasarar Diri.

Kara karanta wannan

Kogi: Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan APC, ta jero dalilai

Gwamna Diri da Sylva.
Kotun ƙoli ta kori karar da Sylva ya kalubalanci nasarar Gwamna Douye Diri Hoto: Douye Diri, Timipre Sylva
Asali: Facebook

Mai shari'a Mohammed Lawal shi ne ya karanto hukuncin kotun a madadin kwamitin alkalai biyar yau Jumu'a, 23 ga watan Agusta, 2024, The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya yanke hukuncin cewa ƙarar da Sylva ya ɗaukaka mai lamba SC/CV/648/2024, ba ta cancanta ba.

Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin baya

Kotun ƙolin ta kuma tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a baya, wadda ta ce tsohon ministan ya tafka kuskure a ƙarar da ya ɗaukaka.

A cewar kotun, Sylva ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Bayelsa da aka kammala ya saɓa doka ta hanyar shigar da kara fiye da ɗaya kan hukuncin kotun zaɓe.

Wannan ya sa kotun ƙoli ta kori karar Timipre Sylva, sannan ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP, kamar yadda Channels ta kawo.

Kara karanta wannan

CJN: Alkalin Alkalan Najeriya ya bar aiki a gwamnati, bayanai sun fito

Tun farko dai hkumar zaɓe INEC ta bayyana Gwamna Diri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe da ƙuri'u 175,196.

Zanga-zanga ta ɓalle a Jigawa

A wani rahoton kuma wasu gungun mutane daga ƙaramar hukumar Ringim sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Jigawa da ke Dutse ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamna Umar Namadi ya tsige kwamishinan noma, Muttaka Namadi wanda ya fito daga yankin Ringim.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262