Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauki Matakin Tabbatar da Ƴancin Kananan Hukumomi a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutum 10 da zai sa ido da tabbatar da an aiwatar da hukuncin ƴancin ƙananan hukumomi
- Sakataren gwamnati, George Akume ne zai jagoranci kwamitin wanda ya ƙunshi ministoci, gwamnan CBN da kuma gwamnonin jihohi
- Aikin da ya rataya a wuyan kwamitin shi ne tabbatar da ƙananan hukumomi na gudanar da harkokinsu ba tare da wani katsalandan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutum 10 domin tabbatar da hukuncin kotun ƙoli na ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya.
Idan ba ku manta ba ranar 11 ga watan Yuli, 2024, kotun koli ta yi hukuncin ƴantar da ƙananan hukumomi kuma ta umrci a riƙa tura masu kuɗinsu kai tsaye daga tarayya.
Wannan ya sa gwamnatin karkashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kafa kwamitin da zai sa ido tare da tabbatar da an yi biyayya ga umarnin kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da naɗa kwamitin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X yau Talata.
'Yan kwamitin ƴancin kananan hukumomi
Jami'in hulɗa da jama'a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen ya ce Sanata George Akume ne zai jagoranci kwamitin.
'Yan kwamitin sun haɗa da ministan kuɗi, Antoni Janar kuma ministan shari'a, ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Akanta-Janar da gwamnan babban banki CBN.
Sauran su ne babban sakataren ma'aikatar kuɗi, shugaban hukumar tattara kuɗin shiga, gwamnonin jihohi da wakilan ƙananan hukumomi.
Wane aiki aka ɗorawa kwamitin?
“Kwamitin zai maida hankali wajen tabbatar da ba kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu da ba su damar gudanar da aiki yadda ya kamata ba tare da gwamnoni sun masu katsalandan ba.
"Hakan wani ɓangare ne na yunƙurin shugaban kasa Bola Tinubu wajen tabbatar da bin kundin tsarin mulki sau da ƙafa," in ji sanarwar.
Gwamna Ododo ya naɗa hadimai 1,192
A wani rahoton kuma, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya naɗa sababbin hadimai 1,192 waɗanda suka fito daga faɗin kananan hukumomin jihar Kogi.
Sakatariyar gwamnatin Kogi, Dr. Folashade Ayoade ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, ta ce za su fara aiki ranar 1 ga watan Satumba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng