Gwamna a Arewa Ya Duba Matsin da Ake Ciki, Ya Naɗa Mutane Sama da 1,000 a.Muƙamai
- Gwamna Ahmed Usman Ododo ya naɗa sababbin hadimai 1,192 waɗanda suka fito daga faɗin kananan hukumomin jihar Kogi
- Sakatariyar gwamnatin Kogi, Dr. Folashade Ayoade ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, ta ce za su fara aiki ranar 1 ga watan Satumba
- Waɗanda gwamnan ya naɗa sun haɗa da manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman a gundumomi da kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya amince da nadin karin hadimai 1,192.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar Kogi Dr Folashade Ayoade ta fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, 2023.
Sanarwan ta ce Gwamma Ododo ya amince da naɗin Yakubu Abdulhakeem a matsayin babban sakataren hukumar kula da naƙasassu ta jihar Kogi, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya naɗa SSA da SA
Ahmed Ododo ya kuma naɗa manyan masu taimaka masa na musamman (SSA) 166 da kananan mataimaka na musamman (SA) 36.
Sanarwar ta ce:
"Hadiman da gwamna ya naɗa sun hada da Yakubu Abdulhakeem a matsayin Babban Sakatare, ofishin nakasassu na jihar Kogi, da manyan mataimaka na musamman 165, da mataimaka na musamman 36.
"Sauran waɗanda gwamnan ya naɗa sun haɗa da hadimai 574 na gundumomi da masu taimakawa na musamman 29 a kananan hukumomin jihar Kogi."
Ododo ya naɗa haɗimai a ofishin matarsa
Alhaji Ahmed Ododo ya kuma amince da nadin Alhaji Ibrahim Abdulsadiq a matsayin Darakta a ofishin uwar gidan gwamna da da wasu hadimai.
Gwamnan ya taya daukacin wadanda suka samu muƙamai murna, sannam ya buƙaci su yi iya bakin kokarinsu wajen yiwa al'umma hidima da kawo ci gaba a Kogi.
A ƙarshe sakatariyar gwamnatin ta ce dukkan waɗannan naɗe-naɗe za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2024.
Zaben Kogi: Kotun koli za ta raba gardama
A wani rahoton kuma kotun koli ta tanadi hukunci a karar da Murtala Ajaka dan takarar SDP ya shigar na kalubalantar nasarar Usman Ododo a zaben Kogi.
Ajaka ya daukaka kara kan hukuncin dakotun zabe ta yi na tabbatar da zaben Ahmed Usman Ododo na APC a matsayin gwamnan Kogi.
Asali: Legit.ng