Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Shirin Tsige Ganduje Daga Mukamin Shugabancinta

Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Shirin Tsige Ganduje Daga Mukamin Shugabancinta

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa akwai shirin tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancinta
  • Mataimakin sakataren tsare-tsare na ƙasa na APC, Nze Chidi Duru ya bayyana cewa ko kaɗan babu shirin raba Ganduje da muƙaminsa
  • Martanin na APC na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin sauke shi daga kan muƙamin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta fito ta yi magana kan batun karɓe shugabancinta daga hannun Abdullahi Umar Ganduje.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu na shirin raba Ganduje da shugabancin APC saboda zarge-zargen da ake yi masa kan cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 da aka ƙulla da nufin wargaza shirin tazarcen Bola Tinubu a 2027

APC ta musanta batun tsige Ganduje
Jam'iyyar APC ta ce babu batun tsige Ganduje daga mukaminsa Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Sai dai, a yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch, mataimakin sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam'iyyar APC, Nze Chidi Duru, ya bayyana raɗe-raɗin a matsayin abin dariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me APC ta ce kan shirin tsige Ganduje?

Nze Chidi Duru, ya bayyana cewa sauya ragamar shugabancin jam’iyyar zai iya kawo rashin daidaito a cikinta.

"Shugabancin jam'iyyar zai kasance mara daidaito. Dole a ce akwai daidaito ko da wajen gudanar da shugabancin jam'iyyar. Masu batun cire shi mafarki kawai suke yi."
"Ban san cewa ko haka ya kamata a ce ana gudanar da jam'iyya ba. Ba a gudanar da jam'iyya ba tare da daidaito ba. Abubuwa za su lalace."
"Shugabancin jam'iyyar an kai shi yankin Arewa maso Yamma. Wannan ita ce matsayar da aka cimmawa a wajen taron NEC wanda ya samu halartar dukkanin ƙusoshin jam'iyyar."
"Idan har akwai wanda ya ji bai gamsu da hakan ba, kamar yadda na saba faɗa cewa muna bin doka da oda, yana da ƴancin zuwa kotu."

Kara karanta wannan

Jihar Kudu ta nemi daukin shugaban APC Ganduje domin ceto siyasar Tinubu a 2027

- Nze Chidi Duru

Jigon APC ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC, Jesutega Onokpasa, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara kan hanyar gyara Najeriya.

Jesutega ya shawarci Tinubu da ya samar da ƙwararrun ƴan Najeriya a kusa da shi domin ya samu damar gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi da kuma cimma tsare-tsarensa kan tattalin arziƙin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng