Sabon Ɗan Majalisar PDP da Aka Rantsar Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Sauya Sheka

Sabon Ɗan Majalisar PDP da Aka Rantsar Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Sauya Sheka

  • Ɗan majalisar dokokin jihar Abia wanda ya kama aiki kwanan nan ya maida martani kan raɗe-raɗin yana shirin ficewa daga PDP
  • Hon. Aaron Uzodike ya bayyana cewa ba shi da shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa Labour Party a halin yanzu
  • Jim kaɗan bayan rantsar da shi, aka fara yaɗa jita-jitar cewa gwamnatin Abia ta tilasta masa sa hannu a yarjejenuyar komawa LP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Sabon ɗan majalisar dokokin jihar Abia da ya kama aiki kwanan nan karkashin inuwar PDP, Aaron Uzodike ya mayar da martani kan raɗe-raɗin zai koma LP.

Ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, aka rantsar da Hon Uzodike na jam'iyyar PDP bayan tsawon watanni yana dako a jihar da ke Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Malami ya faɗi wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa idan PDP ta fito da Atiku a 2027

Aaron Uzodike.
Sabon dan majalisar dokokin jihar Abia da aka rantsar da musanta shirin komawa LP Hoto: Hon Aaron Uzodike
Asali: Facebook

Yadda kotu ta ba 'dan majalisar nasara

Uzodike ya fafata a zaben ɗan majalisar jiha mai wakiltar Abia ta Arewa, amma ya sha kaye a hannun Destiny Nwangwu na LP, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka ya garzaya kotun daukaka kara da ke jihar Legas, inda kotun ta soke zaɓen ɗan takarar LP tare da ayyana shi (Uzodike) a matsayin wanda ya yi nasara.

Rantsar da Uzodike a majalisa

Duk da hakan shugaban majalisar dokokin Abia, Hon. Emmanuel Emeruwa, ya ki rantsar da Uzodike bayan hukuncin da kotu ta yanke na cewa shi ne ya ci zaɓe.

Jim kadan bayan rantsar da shi, aka fara rade-radin cewa gwamnatin Abia ta tilasta masa sanya hannu kan yarjejeniyar komawa jam’iyyar LP daga baya.

Ɗan majalisar na shirin komawa LP?

Amma da yake hira da Premium Times a ranar Alhamis, dan majalisar ya ce babu wata yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin jihar ta sauya sheka zuwa LP.

Kara karanta wannan

Naira ta yunƙuro, ta yi raga raga da Dalar Amurka a kasuwar canji ta Najeriya

"Ba mu yi wata jarjejeniya ba kuma ba ni da niyyar sauya sheka zuwa LP a halin yanzu," in ji shi.

INEC ta tabbatar da sahihancin zaɓen 2023

Ku na da labarin INEC ta bayyana cewa babu wani tuntuɓen alkalami ko ruɗani a sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2023.

Hukumar INEC ta jaddada cewa sakamakon zaɓen da aka ji daga bakinta bayan kammala kaɗa kuri'u a 2023 sahihi ne kuma ingantacce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262