Manyan Yan Siyasa, Tsofaffin Hadiman Ganduje Sun Kafa Kungiya da Manufa 1 a Kano
- Jiga-jigan APC da suka riƙe mukaman siyasa a gwamnatin Ganduje sun kafa sabuwar kungiya da manufa guda a jihar Kano
- Shugaban ƙungiyar kuma tsohon manajan darakta na hukumar ruwa ta Kano ya ce tuni suka fara raba tallafin buhunan shinkafa ga mabukata
- Ya ce sun kafa kungiyar da ta kunshi tsofaffin kwamishinoni, ƴan majalisa da hadiman Ganduje da nufin kawar da fatara a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Manyan ƴan siyasa da suka riƙe muƙaman siyasa a matakin jihar Kano da ƙasa sun haɗa sabuwar kungiya domin kawar da fatara da yunwa.
Jiga-jigan na APC waɗanda mafi akasarinsu sun riƙe muƙamai a gwamnatin Abdullahi Ganduje sun raɗawa ƙungiyar sunan, 'APC Strong Forum'.
Kano: Kungiyar ta fara raba buhunan shinkafa
Sabuwar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin tsohon Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Dokta Garba Ahmad, ta raba buhunan shinkafa 2,481 mai nauyin kilogiram 10 a jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba Ahmad shi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano ranar Laraba, kamar yadda Leadership ta kawo.
Ya bayyana cewa babban daraktan hukumar samar da wutar lantarki ta kasa Abba Ganduje ne ya bayar da tallafin shinkafar domin taimakawa kungiyar wajen gudanar da ayyukanta.
Manyan ƴan siyasar da suka kafa ƙungiyar
Tsohon daraktan ya ce:
“Ƙungiyar da muka kafa ta kunshi tsofaffin masu rike da mukaman siyasa na APC a Kano, wadanda suka hada da kwamishinoni, manajoji, mataimaka na musamman, ‘yan majalisa, da sauran su.
"Mun raɗa mata suna APC Strong Forum wadda ta kunshi dukkan waɗanda suka rike mukaman siyasa kamar yadda na ambata a karkashin tsohuwar gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.
"Don haka mun kafa wannan ƙungiya ne domin mu taimaka wajen rage radadi da wahalhalun rayuwa da talakawa ke fuskanta a jihar Kano ba tare da la’akari da ɓangaren siyasa ba."
Gwamna ya magantu kan takara a 2027
A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce Goodluck Jonathan zai iya dawo da Najeriya kan turba mai kyau idan ya koma kan mulki.
Da yake martani kan kiraye-kirayen ya fito takara a 2027, gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take amma ba zai kara da migidansa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng