Gwamna Ya Jingine Atiku, Ya Faɗi Mutum 1 da Ya Kamata Ya Karɓi Mulkin Najeriya a 2027

Gwamna Ya Jingine Atiku, Ya Faɗi Mutum 1 da Ya Kamata Ya Karɓi Mulkin Najeriya a 2027

  • Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce Goodluck Jonathan zai iya dawo da Najeriya kan turba mai kyau idan ya koma kan mulki
  • Da yake martani kan kiraye-kirayen ya fito takara a 2027, gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take amma ba zai kara da migidansa ba
  • Kauran Bauchi ya buƙaci ƴan Najeriya su lallaba tsohon shugaban kasa Jonathan ya sake tsayawa takara idan za ayi zaben 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce yana da ƙwarin guiwar cewa Goodluck Jonathan zai ba da mamaki idan ya koma kujerar shugaban kasa.

Gwamnan ya tuna irin ci gaban da Najeriya ta samu a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Jonathan.

Kara karanta wannan

Shekarau ya bayyana wani babban sirrinsa kafin ya zama gwamnan Kano

Goodluck Jonathan.
Gwamnan Bauchi ya yabawa Jonathan, ya ce shi ya dace da mulkin Najeriya Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Getty Images

'PDP ta kawo ci gaba a Najeriya'

Bala Mohammed ya yaba da nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a tsawon lokacin da ta ɗauka kan madafun iko, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙauran Bauchi ya ba da misali da gudunmawar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar a fannin sadarwa, noma, da gina ababen more rayuwa.

"Hanyoyin motocin da muke da su a yankin Arewa maso Gabas duk a zamanin Obasanjo aka gina su," in ji Mohammed.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin da yake mayar da martani ga wata kungiya mai zaman kanta ta bukaci ya duba yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Bala Mohammed ya gindaya sharaɗin tsayawa takara

Gwamna Bala Mohammed ya tabbatar da cewa ƙofarsa a buɗe take ta neman shugabancin ƙasar nan matukar dai Jonathan ba zai tsaya takara ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya kare matakinsa na sukar Tinubu, ya yi jawabi mai kyau

“Game da kiran da kuka yi mani, har yanzu ina tunanin damata a matsayina na jagoran ‘yan adawa. Na san akwai shugabanni na gari a cikin PDP, musamman maigidana Goodluck Jonathan.
“Na sha nanata cewa muddin Jonathan yana nan, ba zan nemi shugabancin kasar nan ba, sai dai idan ya yanke shawarar ba zai tsaya takara ba."
"Idan har za mu iya lallashinsa ya fito, zan goyi bayansa da jinina. Ina fatan za ku hadu da shi ku lallaba shi ya sake fitowa takara.”

- Gwamna Bala Mohammed.

Gwamnan Bauchi ya soki mulkin Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ɗora laifin halin ƙuncin rayuwar da ake ciki kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu.

Sanata Bala ya ce tsare-taren tattalin arziƙi na gwamnatin APC ne ya kawo ƙunci, yunwa da wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262