Yan Sanda da Matasa Sun Mamaye Sakatariyar Jam'iyyar APC, Bayanai Sun Fito
- Rahotanni sun nuna ƴan sanda da wasu matasa sun kewaye babban sakatariyar APC ta jihar Benuwai a Makurɗi
- Wannan ne karo na huɗu da aka kulle sakatariyar tun bayan darewar APC gida biyu a jihar da ke Arewa ta Tsakiya
- Jami'an tsaro sun ɗauki matakin kulle wurin ne yayin da ɓangarori biyu suka shirya gudanar da taruka yau Alhamis, 15 ga watan Agusta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - 'Yan sanda da matasa sun kewaye sakatariyar jam'iyyar APC a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai, sun garƙame ta da kwaɗo.
Wannan shi ne karo na huɗu da aka kulle babbar sakatariyar APC reshen jihar Benuwai a wannan shekarar da muke ciki.
Meyasa jami'an tsaro suka kulle ofishin APC?
Hakan na zuwa ne gabannin taron kwamitin gudanarwa na jiha (SEC) karkashin jagorancin shugaban tsagin APC, Austin Agada, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Agada da sauran shugabannin APC na tsaginsa a jihar Benuwai sun shirya gudanar da taron SEC yau Alhamis, 15 ga watan Agusta, 2024.
A ɗaya ɓangaren kuma tsagin APC karƙashin Benjamin Omakolo ya shirya gudanar da taro yau, wanda hakan ya ci karo da tsagin Agada.
Benjamin Omakolo ya kira wannan zama ne domin tattaunawa kan yadda jam'iyyar APC za ta shirya tunkarar zaɓen kanann hukumomi mai zuwa a jihar.
Gwamna Alia ya gargaɗi tsagin Agada
Ana cikin haka ne aka ji Gwamna Hyacinth Alia na gargaɗin tsagin Agada da cewa duk abin da ya biyo baya su kuka da kansu idan suka gudanar da taron da suka shirya yau.
Gwamna Alia ya yi wannan gargaɗin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Tersoo Kula ya fitar, Daily Trust ta rahoto.
Yanzu haka dai jami'an tsaro sun yi wa sakatariyar APC kawanya tare da toshe dukkan titunan yankin, inda matasa ɗauke da sanduna suka karkatar da masu ababen hawa zuwa titin tashar jirgin ƙasa.
Hycinth Alia ya roki matasan Benue
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Benuwai ya yi kira da roƙo ga matasa su daina shiga ayyukan laifi, su rungumi zaman lafiya domin samun ci gaba
Hyacinth Alia ya bayyana cewa duk wani ƙoƙari da gwamnati ke yi domin gyara goben matasa ne,ya roki su kama hanya mai ɓullewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng