Jam'iyyar APC ta Sake Magana kan Mukamin Sanata Ali Ndume a Majalisa

Jam'iyyar APC ta Sake Magana kan Mukamin Sanata Ali Ndume a Majalisa

  • Jam'iyyar APC ta sake magana kan yiwuwar dawo da Sanata Ali Ndume mukaminsa na mai tsawatarwa a majalisa
  • APC ta tabbatar da cewa ta fara magana da shugabannin majalisar dattawa kan dawo da Sanata Ali Ndume kan matsayinsa
  • Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata Ali Ndume ne bisa kalamai da ya yi a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta bayyana ƙoƙarin da ta fara kan dawo da Muhammad Ali Ndume matsayinsa a majalisa.

Hakan na zuwa ne bayan Ali Ndume ya ba jam'iyyar APC hakuri kan kalaman da ya fada a kan shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Dan Majalisar NNPP ya gargadi Tinubu, APC kan illar Alhassan Doguwa

Sanata Ai Ndume
APC ta sake magana kan Sanata Ndume. Hoto: Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wani jigo a APC ya bayyana mata kokarin da suka fara kan ganin Ali Ndume ya koma matsayinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Ndume: APC ta tattauna da majalisa

Wata majiya ta bayyana cewa a yanzu haka jami'yyar APC ta fara tattaunawa da majalisar dattawa kan tabbatar da cewa Ali Ndume ya dawo matsayinsa.

APC ta tabbatar da fara maganar ne kwanaki kadan bayan Sanata Ali Ndume ya gana da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaba a APC ya yi maganar Ali Ndume

Mataimakin shugaban tsare tsare na jam'iyyar APC na kasa, Nze Chidi Duru ya ce sun fara magana kan Ali Ndume.

Sai dai Nze Chidi Duru ya ce tattaunawarsu da majalisa ba za ta kasace a bayyane ba ta inda mutane za su san halin da ake ciki.

Duru: 'Majalisa ce za ta yi hukunci'

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

Chidi Duru ya ce duk da za su yi kokarin tuntubar majalisa kan Ali Ndume, yan majalisar ne kawai za su iya dawo da shi.

Nze ya kara da cewa duk da ba su da tabbas dari bisa dari kan dawowar Ali Ndume matsayinsa, suna da karfin gwiwa a kan yan majalisar za su girmama buƙatar jami'yyar.

Zaben Edo: APC ta yi taro a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da shirye-shiryen yadda za ta karɓe mulkin wasu jihohi a Kudu .

Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a wani Otal da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng